Connect with us

SIYASA

Zaben 2019: ‘Yan Kasuwa Za Su Tsaida ‘Yan Takarkarunsu A Kano

Published

on


Daga Abdullahi M. Sheka, Kano

Sama da shekara saba’in Kano ke rike da kambun cibiyar cinikayya a lardin Arewacin Sahara, kuma jihar ce ke zaman sansanin da ya dara kowanne karbar bako daga duk inda ya fito a duniya, wannan ta sa a kullum ‘yan kasuwa ke kara nutsuwa da mu’amala da Kanawa. Sakamakon daukar wancan tsawon lokacin da Kano ta yi tana rike da wannan kambu duk mai kyakkyawan tunani zai zaci duk gwamnatin da ta zo mulkar Kanawa  za a samu kyakkyawan wakilcin ‘yan kasuwa domin kare kimar kasuwanci da ‘yan kasuwa. Haka kuma an yi ittifaki kashi saba’in da biyar cikin dari na daukacin abubuwan da ake bukata da ya shafi harkar takara har zuwa gudanar da zabuka daga hannun ‘yan kasuwa ke fita, walau kudi wanda da harajin da suke bayarwa gwamnati ke tinkaho ko kuma yawan al’ummar ‘yan kasuwa.

Da farko dai kowa ya aminta da cewar kaso mai tsoka ne ke fitowa ta fuskar haraji daga ‘yan kasuwa, kuma idan aka dubi Jihar Kano kasuwanni nawa ne ake gudanar da kasuwanci a duk ranar Allah Ta’ala, kuma nawa ake samu ta fuskar haraji a wadanann kasuwanni, sannan kuma me aka yi wa kasuwannin ko ‘yan kasuwar ko ma harkar kasuwancin baki daya? Wannan tambaya ita ‘yan kasuwa suka kasa samun amsarta tsawon lokaci. Ko da kuwa wakilci a ka zo bayarwa na ‘yan kasuwa sai ka ga gwamnatoci ko dai a dauko wanda ko sayayya ba ta kai shi kasuwa ko kuma a dauki dan kasuwar riga wanda ba shi da wata alaka da kasuwanci idan ka cire bukatar kansa. Akwai bangarori da ya kamata a ce ‘yan kasuwa ne ki wakiltar ‘yan kasuwa da kasuwanci a kunshin mukaman da gwamnatoci ke samarwa. Misali, kwamishinan ma’aikatar kasuwanci da cinikayya, mashawarci kan harkokin kasuwanci, cibiyar cinikayya da masana’antu da dai sauransu. Kamata ya yi a ce duk wadannan mukamai ‘yan kasuwa aka damka wa alhakin bayar da wanda ya san kimar kasuwanci da ‘yan kasuwa.

Haka kuma, duk al’amari idan ya taso sai ka ji ana rajin tallafa wa ‘yan kasuwa ko kuma harkar kasuwanci, amma daga lokacin da aka gama kwazazaton shi kenan sai ka ji shiru kamar an shuka dusa, abin da ke faruwa kenan a duk lokacin da wata annoba ta afka wa ‘yan kasuwa, gwamnatoci kan kafa kwamitoci domin samar da wani tallafi amma a karshe sai ka ji ba wani sakamakon alheri da ya biyo baya. A duk lokacin da gwamntoci suka shelanta yin wani gyara a kasuwanni, ko dai samar da sabbin gine-gine ko hanyoyi, sai ka ji wasu rukunin jama’a sun shigo kasuwa suna bada umarni ‘yan kasuwa su tashi za su fara aiki, karshe idan batun rumfuna ne idan aka kammala aikinsu wadanda ake fara rabawa wani ma ko kasuwar bai taba shiga ba, karshe sai ka ga an durkusar da ‘yan kasuwa masu karamin karfi. Wannan ya faru a kasuwar Sabon Gari da kasuwar Kantin kwari da ta Kofar Wambai da sauransu, da yawa yanzu haka akwai ‘yan kasuwar da suka yi tagumi sakamakon irin wancan salon wakilcin da bashi da wata alaka da ‘yan kasuwa.

Ire-iren wadannan dalilai suka sa wasu matasan ‘yan kasuwa yin karatun-ta-nutsu domin yi wa matsalar kallon tsanaki, inda a karshe suka fahimci duk wani taimako da kake son yi wa dan’uwanka, ko abokin san’arka, ko kuma kasuwancin naka, tun da lokacin demokuradiyya ake ciki, sannan kuma kundin tsarin mulkin kasar nan ya bai wa kowa damar shiga zabe a zabe shi. Ta wannan hanya ce kadai za ku zabi wanda yasan darajarku da ta sana’arku,  kuma wanda yasan ciwon sana’ar da masu yin ta, haka kuma shi ya san hanyoyin inganta ta kamar yadda masu iya magana ke cewa, ‘mai daki shi ya san wurin da ke masa yoyo’.

Bayan dogon nazari, tuntuba da kuma ganawa da manyan ‘yan kasuwa da duk masu ruwa da tsaki a cikin harkokin kasuwanci a Jihar Kano, rukunin wadannan matasan ‘yan kasuwa suka yanke shawarar kafa zauren ‘yan kasuwa da kyakkyawan  shugabanci, wato Traders Peace Forum and Good Gobernace a Turance domin tsunduma cikin harkokin siyasa domin samar da kyakkyawan wakilci a kunshin gwamnatin da ake sa ran kafawa a kakar zaben shekara ta 2019.

Tuni shirye-shirye sun yi nisa ta fuskar tattaunawa tare da samar da manufofin ‘yan kasuwa a kan tubalin da za a dora tafiyar a kanta, guda cikin masu ruwa da tsaki a harkar kawo sauyi cikin tsarin kasuwanci a jihar kano, Alhaji Ibrahim Waru ya bayyana cewa, babban makasudin samar da wannan sabon zaure shi ne domin kawo ci gaban da muka jima muna jira, amma rashin ingantaccen wakilci daga bangaren masu rike da madafun iko ya sa kullun muke tubka baya na warwarewa. Sai kuma dalilinmu na biyu wanda shi ne, samar da hanyoyin da za mu kawo gyara tare da cikakken ‘yancin dan kasuwa da kasuwanci, shirin sauya tsarin kasuwanci domin tafiya dai-dai da zamani, tabbatar da hadin kan ‘yan kasuwa na hakika domin yin magana da murya guda.

Alhaji Ibrahim Waru ya ce, mun gaji da turin motar alfa kullum rami take jefa ‘yan kasuwa, dubi yadda kullum ake yi wa ‘yan kasuwa abin da aka dama da sunan haraji, ya ce ba wanda ya fi dan kasuwa biyan haraji, amma kullum an mayar da mu saniyar tatsa. Saboda haka yanzu gaskiya tura ta kai bango, ‘yan kasuwa mun tsaya wuri guda domin nema wa kanmu mafita. Wanda duk ya san yadda zabe ke gudana ya tabbatar da cewa wurin ‘yan kasuwa ake zuwa neman taimakon kudi,  muke da kaso mai tsoka na masu kada kuri’a,  mu ke bayar da kashi 70% na gurabun aiki ga matasan da ba wata gwamnati da ke iya samar da wannan gurabun ma’aikatan. Amma a ce wakilci ma an gagara yi wa ‘yan kasuwa adalcin bai wa dan kasuwa ire-iren wannan mukamai. Yanzu lokaci ya yi da ‘yan Kasuwa suma za su fito domin bayar da irin tasu gudunmawar kamar yadda kundin tsarin mulki ya bai wa duk wani dan kasa.

Yanzu haka dai shirye-shirye sun yi nisa na ganin ire-iren mukaman da ‘yan kasuwa za su nema, ciki kuwa za su fara tun daga matakin kansila har zuwa kujerar gwamna, kuma ‘yan kasuwar sun samar da jagoranci domin tabbatar da ba a yi wa shirin sakiyar da ba ruwa ba, an tsara yadda za su samar wa kansu kudaden gudanar da wannan harka, da kuma tsarin yi wa duk wanda suka tsayar takara kamfen tun daga mazabarsa, shugabancin ‘yan kasuwa zai je har mazabar dan takarar nasu su shaida wa jama’a ga nasu kuma ga dalilansu.

Babu shakka wannan babban kalubale ne ga masu rike da madafun ikon da a baya suka mayar da ‘yan kasuwa gugar yasa, sannann kuma irin wannan juyin-juya-halin an jima da fara amfana da shi a duniya. Yanzu dai abin da ya rage shi


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI