Connect with us

NAZARI

Da Gaske Akwai Zinare A Kan Masu Sanko?

Published

on


Daga Daga Wakilinmu

Allah daya gari bamban, a yayin da al’ummarmu ta Nijeriya musamman hausawa ke alakanta sanko da arziki ko tarin ilimi. Su kuwa a kasar Mozambikue abin ba haka bane. Matukar ma kana da sanko a kanka, sai dai ka shiga taitaiyinka tare da taka-tsantsan din wuraren da zaka rika zuwa.

A wata sabuwa, ‘Yan sanda a kasar Mozambikue sun gargadi masu sanko cewa matsafa ‘yan yankan kai na iya far musu, bayan kisan mutum biyar a baya-bayan nan don cire sassan jikinsu.

An kama mutum biyu da ake zargi a tsakiyar lardin Milange, inda kashe-kashen suka faru.

Kwamandan ‘yan sandan lardin Zambezia da ke tsakiyar Mozambikue, Afonso Dias ya ce: “Sun yi imani cewa akwai zinare a cikin kan mutumin da ke da sanko.”

Haka kuma a wani rahoton makamancin wannan, an kakkashe zabiya ma a yankin don yin tsafi da sassan jikinsu. A cikin makon jiya kadai, an kashe mutum uku.

Sai dai hukumar ‘yan sanda ta yi watsi da batun wai akwai zinare a cikin kan masu sanko. Hukumar ta ce wata yaudara ce ta bokaye don samun mutanen da za su yanko musu kan irin wadannan mutane.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutanen da ake zargi matasa ne guda biyu ‘yan kimanin shekara 20.  Wani mai magana da yawun jami’an tsaron yankin, Miguel Caetano, ya fada wa AFP cewa an yanke kan wani mutum kuma aka datse masa al’aura.

Ya ce wadanda ake zargin sun ce ana amfani da sassan jikin ne wajen yin asiri don samun karuwar arziki ga masu kudin da ke zuwa neman magani daga Tanzania da Malawi.

A shekarun baya-bayan nan an samu kashe-kashen zabiya a yankin Afirka Ta Gabas, inda bokaye suke amfani da sassan jikinsu don yin asiri.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI