Connect with us

RAHOTANNI

Gwamna Masari Yayi Kira Ga Masu Cutar Kanjamau

Published

on


Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina.

Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ja hankali masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (wato SIDA) da su zama masu amana da gaskiya a yanayin mu’amularsu  da zamantakewarsu cikin al’umma.

Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wannan jan hankali ne lokacin da kungiyar masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki suka kai masa ziyara a fadar gidan gwamnatin jihar Katsina.

Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta taimaka wajan ganin  an taimakawa mambobin wannan kungiyar wajan kula da da kuma bada magunguna da za su taimaka masu kwarai da gaske akan wannan lalura da suke dauke da ita.

Gwamna Aminu Bello Masari ya sha alwashi taimakawa kungiyar wajan ganin ta shirya zaban shuwagabaninta inda ya bada tabbacin mika rahotan abubuwan da suke bukata domin gwamnati ta gani ta kuma san abin yi.

Tunda farko da yake nasa jawabin shugaban kungiyar masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki  Malam Shehu Ibrahim ya ce sun zo gidan gwamnati ne domin kawo ziyarar girmamawa da kuma bayyana wasu daga cikin matsalolin da suke fuskanta.

Inda ya bayyana cewa suna da bukatar dauka mataki na so sai akan mambobin su dangane da magunguna da ake ba su, domin kare su daga fadawa cikin wani hali na daban.

Shugaban ya kuma nuna bukatar da kungiyar ke da ita da mota mai daukar mutun goma sha takwas wanda ya ce idan gwamnati ta ba kungiyar zata taimaka wajan cigaba da aikin kungiyar ke yi na fadakar da jama’a dangane da wannan lalura.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI