Connect with us

NAZARI

Tumbin Giwa: Da Ni Ce Mama Taraba…

Published

on


Tare da El-Zaharadeen  Umar 08029073523

Yanayin siyasar Nijeriya kullum sai canza sabon salon ya ke sakamakon yadda abuwabuwan suke kwan gaba kwan baya, wannan ba ya rasa nasaba da yadda ake wasa da hankalin jama’a musamman talakawan da ake jagoranta.

Duk lokacin da ake son wasa da kwakwalen ‘yan Nijeriya to hanyoyi suna da yawa da ake amfani da su, kuma a yi yadda ake so da su a lokacin da ake so bisa yanayin da ake so ba tare da wata tangarda ba, kuma suna ji suna gani suna kuma saurare. Yanzu babbar hanyar da ake amfani da ita wajan daukar hankalin ‘yan Nijeriya ita ce kafar sadarwa ta zamani (wato soshiyar Midiya) wanda aka gano tana da matukar tasirinta  a tsakanin ‘yan Nijeriya musamman masu ta’amuli da kafar sadarwa ta zamani.

A wannan lokacin kuma a siyasar Nijeriya wanda mafi yawan mutane suke yinta ido a rufe, an haramtawa mutum bayyana ra’ayinsa ma damar bai yi daidai da abin da wasu ‘yan tsirarun mutane suke so ba, kana yin wata magana yanzu za a dauki mataki a kanka.

Mama Taraba giwa karya marake, ita ce ta zama kanun jaridun Nijeriya kusan a mako guda ke nan babu wata kafara sadarwa da za a wayi gari bata ce wani abu ba akan ministan harkokin Mata Sanata Aisha Alhassan (Mama Taraba) saboda kawai ta zabawa manya masu ayi daidai ba tare da yin la’akari da cewa tana da ‘yancin yin haka a matsayinta na ‘yar kasa kuma ‘yar siyasa diya da tsohun mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar.

‘’Idan Allah Ya kaimu Shekarar 2019 Kai ne Dan Takarar Shugabana’’; ma’ana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wannan ita ce maganar da Mama Taraba ta yi wanda ya zama baban zunubi a wannan kasa ta Nijeriya kuma ga alama ba za a taba yafe mata wannan babban laifi ba, ko me yasa?

A Nijeriya, kasar da ake tutiya ana yin dimokuradiyya amma sai gashi wani mutum baya da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa, yana cikin gwamnati ko yana wajanta, babban mutum ne ko talaka ne, Sarki ne ko mai rika da mukamin siyasa. Amma idan ka yi tambaya wace doka ce ta hana dan kasa ya yi haka ba wanda zai baka amsa.

Duk wata magana da za ta ci karo da nuna rashin goyon baya ga wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari dole mutum ya kiyayeta ko da kuwa idan ya fada zata fidda wannan kasar daga cikin halin da muke ciki yanzu, ba a bukatar gaskiya daga kowane mutum, abinda nake nufi da gsakiya anan shi ne dole ka nuna goyon baya akan koma menene.

Akwai tarihi na mutanen da suka lura cewa wasu abubuwa na tafiya ba daidai ba, kuma abin da suka iya shi ne su fada ra’ayin bakinsu, sai dai kuma da yawan lokaci ba a kwashewa lafiya, na kwanan nan ita ce Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Alhassan (Mama Taraba) inda ta bayyana ra’ayinta a siyance amma ya zuwa yanzu abin ya zama abin da ya zama, kai ya koma wani laifin da ba a yafe shi a Nijeriya.

Muna ji muna gani wannan maganar da ta yi, tasa mai gidanta wanda ta yi maganar akansa ya amayar da abin da ke cikin ransa inda ya bayyana cewa wannan gwamnatin ta mayar da shi saniyar ware duk da cewa ya bada gaggarumar gudummawa wajen ganin ta dare bisa iko, babu wanda ya musanta hakan.

Kafin nan ya yi wata magana wanda mafi yawan ‘yan Nijeriya suka amince da ita inda ya bayyana cewa fita daga matsin tattalin arziki shi ne dan Nijeriya ya rika cin abinci sau uku a rana, wannan ko shakka babu an yarda da shi, amma da aka ta so masa ba don suna sane da ko wanene shi da yanzu sun sa ya gyara zaman hularsa a siyasa.

A kwanakin bayan mai Martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi ya rika yin maganganu wadanda shi a mahangarsa ya kamata ace an gyara, kuma ya bada misalai da daman gaske, maimakon abi sahun shawarwarwarin nasa, sai ma dai aka rika yi masa bita da kulli tare da fadin cewa ya daina tsoma bakinsa cikin al’amuran siyasa ko da kuwa za su amfani al’umma.

Da ya ki daina irie-iren wadannan maganganu  sai da suka biyo masa ta bayan gida sannan ya ja bakinsa ya rufe saboda tsoron kadda su shiryo wata guguwa da zata iya yin gaba da rawaninsa, karshe ma dai sai da suka fara yunkurin cireshi kafin Allah Ya kwashe shi daga hannunsu.

Wani abin ma shi ne lokacin da mai Martaba Sarkin Kano ya ke bada irin wadancan shawarwarin sai da aka sa daya daga cikin talakawansa  mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya maida masa martani domin dai kawai a nuna masa iyakarsa sannan ya gane cewa ba a bukatar shawarwari irin nasa.

Haka nan kuma mun ga yadda tsohuwa ‘yar gwagwarmaya Hajiya Naja’atu Mohammad  ta fito fili ta fadi ra’ayinta game da wasu abubuwa da take ganin ya kamata ace sun canza sabon tafiya a wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari, sai da aka yi kamar a cinyeta danya, don an son ba kanwar lasa ba ce, kuma wani wanda zai gwanda mata sani da kuma soyayya ga shugaba Buhari.

Amma ba kyaleta suka yi ba, har gobe a wajansu ta aikata baban zunubi kuma ba su yafe mata  ba, sai dai mutane irin Hajiya Naja’atu Mohammad basa tsoron zargin mai zargi amma dai tasan yana da wahala su bari ta rika ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda ta aikata babban laifi kuma bata nemi gafara ba.

Hajiya Aisha Muhammadu Buhari wacce take uwargidansa ce, na daga cikin mutane da suka bayyana ra’ayinsu game da wasu abubuwa da suke kallon ba daidai ba, amma karshe sai da aka sa shi kanshi madugu uban tafiya ya mayar mata da martani domin ana ganin ta yi abin kunya. Duk yadda ka kai ga kusanci da sanayya ga shugaba Muhammadu Buhari baka kai ga matarsa Hajiya Aisha, amma wadanda ba su yafe laifi sai da suka tuhumeta da aikata manyan laifufuka wanda har yanzu ana ganin tasirin maganar da ta yi akan mijinta da wadanda ba su yafe laifi.

To amma, abinda  ake cewa har yanzu shi ne ba a dauki wadancan maganganu da ake yi wa kallon laifufuka ba aka dora su  bisa ma’aunin hankali da shari’a ba sannan a zo da tuhuma, sai dai kawai an zo wani lokacin da baka isa fadin ra’ayinka ba a siyasance ba, inda har zai ci karo da soyayyar shugaba Muhammadu Buhari koda kuwa ra’ayin naka zai kasance wata gudunmawar a cikin gwamnatinsa.

Baya ga haka akwai maganganu da suke masu ma’anawanda na tabbatar idan da za a yi amfani da su da sun taimaka wajan toshe wata matsalar amma da yake magagannun sun fito daga bakin ‘yan siyasa kuma ‘yan adawa ana yi masu kudin goro kawai a jefa su cikin kwandon shara tare fadin cewa makiya Muhammadu Buhari ne.

Da ace ni ke matsayin Ministan Harkokin Mata Sanata Aisha Alhassan (Mama Taraba) zan koma baya in sake karatun ta nutsu da irin abubuwan da suka faru dangane da batun fadin ra’ayi ko na siyasa ko kuma wani daban, in kuma yi duba sosai, in ga abinda ya samu wadanda suka yi magana ta gaskiaya a baya, in auna inga ni menene zai fidda Mama Taraba ga rogo…

Babu shakka wannan ya nuna cewa akwai matsala so sai a cikin kowanne irin al’amari na siyasar Nijeriya sai dai a wannan karon babu bukatar wani ya ce ga yadda za a yi ko kuma ga yadda yake kallon kaza da ka za bai kamata ba, sannan Mama Taraba ta burge jama’a da ta sha ta dubu ta nuna cewa ita ‘yar halak ce kamar sauran ‘ya ‘ya da suka dage kai da kafa cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi laifi ko kuskure ba, kuma wani mutum daga waje ba zai iya cewa komi ba dan har ya gani. Ko ba komi Mama Taraba yanzu ta fita daga mugun tarkon da ke ta binta, duba da cewa ba fa ita kadai ba ce diya ta halsa ga tsohun mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, akwai mutane irin su Malam Garba Shehu da wannan gwamnatin ke amfani da su wajan maida martani ko daukar hankalin ‘yan Nijeriya akan bututuwa masu matukar mahimmanci.

Sannan ita mun ga abin da ya sameta ko yake shirin samunta saboda kasancewar mai gidanta yana son kujerar Shugaban kasa a shekarar 2019. Sannan wannan ya kara mata kwarin gwiwar fadin duk wani abinda take ganin ya saba da ra’ayinta a siyasance, maimakon zura na mujiya tana ji tana gani za a hanata fadin albarkacin bakinta.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI