Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Kano Ta Inganta Kamfanin Samar Da Takin Zamani

Published

on

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Bisa la’akari da daminar da ake ciki  mai girma Gwamna Ganduje ya tabbatar da  farfado da kamfanin gidan gona na KASCO  wanda ya yi fice ta fuskar samar da takin zamani mai inganci. Wannan jawabi ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar gona na Jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a wata ganawa ta musamman da wakilinmu a Kano.

Ya ce a matakin farko, mai girma Gwamna Ganduje ya turaw a wannan kamfani kudi Naira milyan dari biyar domin sayan sinadarin aikin samar da takin zamani, yanzu haka wannan kamfani  ya ci gaba da aiki inda ake sayar da takin kan farashi mai rahusa daga kan naira 5,500.

Haka nan, ya ce gwamnati ta bayar da tirela 484 na takin zamani ga kananan hukumomin jihar Kano 44, tare da cewa a wannan shekarar Gwamnan jihar ya bayar da umarnin yin sassauta farashin takin daga naira 5,500 zuwa 5,000.  Sai kuma tsarin da gwamnatin Kano ta yi don amfani manoman rani inda ta ba su rance mai saukin ruwa.

Da yake tsokaci kan amfanin gonar da jihar Kano ta shahara wajen samarwa, Dakta Gawuna ya ce, akwai gero da dawa da masara da shinkafa da alkama. Sauran sun hada da wake da waken suya da timatir, tattasai da dai sauransu.

Ta bakin kwamishinan, “Ina tabbatar da cewa kasuwanni a wannan shekara za su tumbatsa da kayan abinci, wanda har sai mun sayar wa makwabtanmu a kasashen waje”.

A karshe, Dakta Nasiru Gawuna ya jaddada aniyar Gwamna Ganduje na ganin matasa kowa ya amfana da kyawawan tsare-tsaren wannan gwamnati.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!