Connect with us

LABARAI

‘Sama Da Kashi 17 Na Daliban Bauchi Suka Yi Nasara A WAEC Da NECO’

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Gwamnan Bauchi Muhammad Abudullahi Abubakar, ya bayyana cewar gwamanatinsa ta bai wa harkar ilimin matasan jihar fifiko da kuma inganta rayuwarsu. Ya ce gwamnatin nasa ta zo da shirye-shirye masu ma’ana wadanda za su inganta rayuwar matasa musamman a kan harkar ilimins.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin wani gangamin nuna goyon baya da kuma neman tallafinsa da kungiyar dalibai (NUBASS) ta kai masa a gidan gwamnatin jihar a kwanakin baya.

Ya ce kafin darewarsa karagar mulkin jihar, harkar ilimi da kuma cin jarrabawar dalibai a bayyane yake cewa dalibai ba su samun nasarar da ta dace sabanin yadda lamarin yake a gwamnatinsa.

“A lokacin da muka amshi ragamar mulki, mun tarar da sha’anin ilimi a cikin wani hali na kaka-ni-ka-yi, amma cikin ikon Allah daga shekarar 2016 mun fara ganin sakamakon yunkurin da muka yi sabili da cin jarrabawar NECO da WAEC da dalibanmu suka yi a lokacin da muka amshi mulkin jihar nan”. In ji shugaban.

Ya kara da cewa, “A lokacin da muka amshi mulki kashi uku ne kawai cikin dari suke samun nasara a jarrabawar kammala sakandare, sai gas hi a lokacinmu sad a kashi 17.6 da suka samu sakamako mai kyau a jarrabawarsu ta WAEC da NECO a 2016. A wannan shekarar ta 2017 kuma, muna sa ran wannan yunkurin namu zai sake biyan bukata”.

Tun far, gwamnan ya nuna jin dadinsa a bisa yadda daliban suka yi jerin gwano daga sassa daban-daban na jihar suka kawo masa ziyara cikin kwanciyar hankali ba tare da wani yamutsi ba. Daga nan ya bayyana cewar, gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta sha’anin ilimi a jihar yadda ya kamata.

A hannu guda, Makama Babba na Farko ya yi kira ga daliban da su jajirce kan karatunsu a kowani mataki, tare da cewa su tsaya tsayin-daka don ganin sun samu ilimi mai amfani don amfanin rayuwarsu da ma al’umma.

Da yake tofa albarkcin bakinsa, mai tallafa wa gwamnan jihar na musamman kan harkokin dalibai Comrade Najimuddeen Garba, wanda shi ne ma ya jagoranci gangamin nuna goyon bayan, ya shaida wa gwamna cewa sun yi wannan fitowar ne domin su jinjina masa a bisa irin gudunmawa da kokarin da yake yi wa dalibai musamman wajen biyansu tallafin karatu a duk shekara.

Ya kuma nuna jin dadinsu a bisa yadda gwamnan ya inganta kwalejin gwamnatin jihar na ATAP inda ya samar musu da dakin kwanan dalibai da kuma samar wa kwalejin ilimin digiri da ya yi.

Daliban da lamarin ya shafa sun yi amfani da wannan damar wajen kai kokon baransu ga gwamnan na sake fasalin tallafin da ake biyan daliban makarantun Islamiyya da cewar abun da suke samu ya kasa, inda suka roki gwamnan da ya dan kaurara musu kason abin da aka saba ba su.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI