Connect with us

LABARAI

‘Yan Siyasa Na Kokarin Mayar Da Siyasar Gudu Baya — Falasko

Published

on


Daga Muhammad Awwal Umar

Honarabul Murtala Abdullahi Falasko shi ne mataimakin jami’an hulda da jama’a na jam’iyyar APC a karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato, a takaitaccen hirarsa da LEADERSHIP A Yau, ya ce matakin da ‘yan siyasa ke dauka a karamar hukumarsa kokari ne na mayar da hannun agogo baya a siyasan ce.

Honarabul Falasko ya bayyana cewa: “Maganar gaskiya ba abu ba ne mai kyau, domin da ‘yan sisayar sun san abin da suke yi da ba akan dan majalisa za a yi zanga-zangar ba. Domin tun bayan kammala zabukan kananan hukumomi ashirin da biyu cikin kananan hukumomi ashirin da uku da muke da su, sannan mu jama’ar karamar hukumar Gudu da gwamnatin jiha ta gudanar da wannan zabukan amma ba a yi na karamar hukumarmu ba har yanzu kuma ba a ce mana komai ba mu kai biyayya ga shi kantoman riko da maigirma gwamna ya nada mana, da cibgaban suke so da gaske ya kamata ne ‘yan siyasar su tunatar da maigirma gwamna cewar har yanzu fa ba a yi zabe a karamar hukumarmu ba.

“Honarabul  Sani dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Gudu ko a majalisar tarayya yake abin da yake yi yanzu ya can-canci a yaba ma sa. Domin shi mutum ne marar tsoro kuma ya tsaya akan hakkin talaka, amma idan akwai wasu makiya ta bayan fage da ke son ganin bayan karamar hukumar Gudu ta ba zan yi musu ba, abin mamaki da takaici shi ne kujera daya da muke alfahari da shi a wannan majalisar ana mana zagon kasa a kansa.” In ji shi.

Dangane da batun zanga – zangar da kuma abin da Falasko ya fahimta, ya ce;  “Kawai wasu gungun ‘yan siyasa ne ke kokarin mayar da siyasar karamar hukumar Gudu baya, domin a jihar sakkwato mu ne karamar hukuma mafi koma baya, dan ba mu da ‘yan boko kuma ba mu da ma’aikata sai yanzu da dan siyasar nan da ke majalisar jiha Honarabul Sani Yakubu ya zo da irin wannan salon na fadakar da jama’a muhimmancin karatun zamani da aikin gwamnati, amma wannan nasarar da suke ganin zai samu ake son mai da shi baya, in kuma an yi hakan ba shi ne aka mayar ba mu jama’ar Gudu ne ake bakin ci gaban da muke samu.

“Shawarar da ni ke baiwa jama’ar Gudu, kar su yarda da ‘yan a fasa kowa ya rasa, kar su yarda da masu kokarin gurgunta karamar hukumar mu. Sannan ina jawo hankalin gwamnatin jiha kan muhimmancin zaben karamar hukumar Gudu, dan mu ma muna da hakkin kamar kowani dan jihar Sakkwato, maigirma gwamna ya tausaya mana, ya ba mu damar mu ta siyasa mu ma mu taka na mu rawar ganin ga jama’ar mu.” In ji Falasko


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI