Connect with us

KASUWANCI

Na Fara Kasuwancin Carbi Tun Ana Sayarwa Kwabo Daya – Mallam Lawal

Published

on

Sana’ar sayar da carbi, sana’a ce da galibin mutane ke mata kallon karamar sana’a da babu wata riba sosai a cikinta kasancewar ba kullum ake saye ba, hasalima wani sai ya shafe shekaru da dama yana amfani da carbi guda daya.

Sai dai kuma, masu irin wannan tunanin kallon tsoro suke yi wa sana’ar wadda a kan haka ne Shafin Kasuwanci ya niki gari domin zakulo sirrin da ke cikin sana’ar.

Malam Lawal Ibrahim da ke sana’ar sayar da carbi a Babban Masallacin Jumma’a na Titin Kano da ke tsakiyar garin Kaduna, wanda ya shafe sama da shekara 45 yana gudanar da wannan sana’ar, ya bayyana wa wakilinmu cewa a lokacin da ya fara sana’ar farashin carbi bai wuce kwabo daya ba.

“Tun ina dan shekara 20 na fara sana’ar sayar da carbi. A lokacin abin da ake sayar da carbi bai wuce kwabo daya ba.”

Carbi yana daya daga cikin kayan da ake amfani da shi wurin ibada a cikin Addinin Musulunci.

Da aka tambaye shi ko mene ne sirrin rike sana’ar har na tsawon wadannan shekarun masu yawa, Malam Lawal ya ce, “a kowace irin sana’a ana bukatar jari da kuma hakuri. Idan mutum yana da wannan a hankali zai rika samun bunkasa”.

Ganin cewa carbi ba kullum ake sayen shi ba sai lokaci-lokaci, Malam Lawal ya ce duk da haka akwai riba.

“Tabbas akwai riba a sana’ar sayar da carbi, domin da babu riba ai ba za ka zo nan ka same ni ina wannan sana’ar ba”.

Malam Lawal wanda ya ce ya koya wa kaninsa wannan sana’ar ya ce shi ma yana samun abin rufin asiri shi da iyalinsa.

Kana ya ce ya fi samun ciniki a ranakun Juma’a inda yake iya sayar da carbi na kimanin Naira dubu goma idan kasuwa ta bude.

Sai dai kuma ya ce sauye-sauyen da ake samu na gwamnatoci a kasa yana shafar sana’ar, kasancewar kowace gwamnati takan zo da salon da zai iya bunkasa kasuwanci ko akasin haka.

A halin yanzu dai ana sayar da carbi daga kan Naira 100 har zuwa 20,000.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!