Connect with us

RAHOTANNI

Ambaliyar Ruwa Na Cigaba Da Janyo Asarar Rayuka A Kebbi

Published

on


Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi

Wasu rahotanni sun bayyana cewar matsalar ambaliyar ruwa a Jihar Kebbi na ci gaba da zamarwa al’umma barazana ta rasa gidaje da dukiyoyi miliyoyin a kowace shekara, har ila yau, al’umma sun zuba igo domin ganin Gwamatin Tarayya da ta Jiha sun magance balahirar amma lamarin shiru.

Da yawan wadanda bala’in ya rutsa da su suna zaune a makarantun firamarai da sakandarai na garuruwan su. Yayin da a wasu lokutan suke samun tallafi daga hukumomi.

Rahotannin da ke fitowa daga Dolekaina da ke karamar hukumar Dandi, an tabbatar da cewar ambaliyar Ruwa ta mamaye gidajen mutane kimanin 100, da kuma dukiyoyin su na miliyoyin naira.

A cikin wata sanarwa Gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Abubakar Mu ‘azu Dakingari, ya ce gwamna ya ziyarci  yankin  Dolekaina don ganewa idonsa abinda ya faru, ya kuma taya su jaje da addu’ar Allah yak are faruwar hakan nan gaba.

Sanarwar ta kara da cewa gwamna ya umarci fitar da iyalan wadanda ambaliyar ruwan ta shafa, domin gudun kamuwa da cutaka. Har ila yau, ya ce za a kai su wani wuri mafi aminci da kuma tsabta, su samu abinci, ruwan sha, magungunan da kuma tsaro mai inganci.

Baya ga haka, Gwamna Bagudu tare da Marafan Dolekaina, Alhaji Muhammad Bello Suleiman, sun zagaya wurare da yawa da al’amarin ya shafa, inda suka ce a halin da ake ciki matsala ba iya Nijeriya kadai ta tsaya ba, har da kasar Nijar.

Har ila yau, Gwamna Bagudu ya ba da umurni a gudanar da kididdiga don a gano adadin mutanen ke gudun daga Arewa Maso Gabas, sakamakon rikicin Boko Haram, domin su ma a ba samu damar ci gaba da tallafa masu.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI