Connect with us

MAKALAR YAU

Yan Fashi Sun Yi Dirar Mikiya A Gidan Mai, Sun Kwace Kudade A Katsina

Published

on


Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

‘Yan fashi da makami su hudu sun yi dirar mikiya a wani gidan mai, mai suna Dan Marna da ke kan hanyar zuwa Mani a cikin birnin Katsina inda suka yi awon gaba kudadan jama’a.

Shaidun gani da ido sun shaidawa LEADERSHIP A Yau cewar ‘yan fashin sun zo gidan man ne da misalin karfe bakwai da minti arba’in da biyar na dare a ranar Alhamis, inda suka fara harba bindiga wanda haka ya sa kowa ya ji tsoro sannan suka cigaba da karbe kudadan jama’a.

Wani wanda aka yi abin a gaban idonsa a yayin da yake kan wani bene kusa da wajen ya ce, ya lura da ‘yan fashi duk matasa ne kuma sun rufe idonsu da farin kyale domin kar a gane su, kuma a cewarsa, sun kwashe kamar mintuna goma suna karbar kudade.

Ya kara da cewa, “bayan sun kwashe kudadan ma su sai dai a gidan Man suka yi kan mai uwa da wabi, sai da suka kwashe kudadan jama’ar da suka zo shan mai kafin daga baya suka bi hanyar Mani kafin zuwan ‘yan sanda.”

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamari ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Gambo Isah inda ya bayyana cewa jami’ansa sun bi ‘yan fashi amma ba su samu nasarar kama ko daya ba.

DSP Gambo Isha ya kara da cewa motar da aka zo yin fashi da ita, tuni suke nemanta domin suna da rahotannin da ke nuni da cewa ana amfani da wannan mota kirar Honda Cibic Panadol Edtra wajen aikata laifufuka da daman gaske, saboda ana yawan ba su labarin motar  cewa an  yin fashi da ita  a wasu wurare.

Ya ce tuni jami’ansu suka baza komarsu domin ganin sun cafke su, kuma suna kira ga jama’ar gari da su taimaka masu da bayani da zarar sun sake haduwa da wannan mota wanda ya bada misalin da cewa daga bayanta akwai alamun kamar ana gyaranta.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahota ba a tabbatar da adadin kudadan da ‘yan fashin suka karbe daga hannun masu sai dai mai, da kuma wadanda suka zo sayan Mai ba.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI