Connect with us

KASUWANCI

Yunkurin Gwamna Badaru Don Bunkasa Kasuwanci A Jigawa

Published

on

Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse

Jihar Jigawa ta kasance daya daga cikin jihohi a wannan kasa Nijeriya wadda Allah ya huwacewa albarkatun kasa bila’adadun, tarin al’umma gamida kyakkyawan yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali, wadda wadannan muhimman abubuwa sune gimshikin habaka da bunkasar kowanne irin kasuwanci a wannan Duniya.

Haka kuma gwamna mai mulki a halin yanzu Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ya kasance hamshakin dan kasuwa kafin darewarsa karagar mulkin jihar wadda hakan ya kara baiwa al’ummar jihar wani kwarin gwiwa na musamman kan zatonsu na bunkasar kasuwanci a wannan jiha karkashin wannan gwamnati.

Dangane ga wadanda ba al’ummar jihar ba kuwa a kullum sun zuba idanu ne kawai tareda tunanin cewa lallai babu shakka jihar Jigawa nan bada dadewa ba zata zama daya daga cikin manyan jihohin arewancin wannan kasa da zasu kasance gaba-gaba a fannin kasuwanci, domin a kullum tunaninsu shi ne dan kasuwa yazama gwamna a jihar da Allah ya huwacewa albarkatun kasa da kyakkyawan yanayin zaman lafiya.

Haka kuma shi kansa gwamnan kafin darewarsa karagar mulkin jihar, bunkasa harkokin kasuwanci da fannin noma na daya daga cikin dumbin alkwaran da ya sha alwashin cimma matukar al,ummar jihar sun ara masa irin wannan dama da suka damka masa a hannunsa a halin yanzu.

Gwamnan ya kuma sha alwashin samarda ayyukan yi ga dubban matasan dake jihar ta Jigawa ta hanyar bunkasa  kasuwanci da kuma fannin noma a jihar baki daya.

Darewarsa kan karagar gwamnan jihar ke da wuya bayan tattaunawa da masu ruwa tsaki gamida masana fannin kasuwan a jihar ta Jigawa, yadda suka ayyana ire-iren damarmakin da jihar keda su a fannin kasuwanci, gwamnan ya dauki matakin farko na bunkasa kananan sana’o’i da kananan masana’antu.

A tashin farko gwamnatin jihar ta Jigawa karkashin jagoran gwamna Badaru ta ware makudan miliyoyin naira yadda ta fito da wani shiri na musamman wadda ya dukufa wajen tallafawa kananan ‘yan Kasuwa.

A lokacin da yake kaddamar da shirin bada tallafin, Gwamna Badaru ya ce gwamnatin ta mika wannan. Kudade ga masu sana’o’in a matsayin tallafi domin su bunkasa sana’o’insu yadda wadansu ma zasu amfana.

Haka kuma ya ce, kafin bada tallafin gwamnati ta dauki dogon lokaci wajen tantance wadanda suka ci moriyar wannan tallafi domin tabbatarda cewa an mika tallafin ga hannun mutanen da suka cancanta ta yadda za’a cimma kudurin da aka sanya a gaba na bunkasa kasuwanci tareda rage zaman kashe wando a jihar.

Alhaji Badaru ya kuma jagoranci wata tawaga ta musamman zuwa kasar Sin yadda gwamnatin jihar ta tattauna da wasu kamfanoni wadanda suka kware wajen hada wayar salula yadda suka amince domin zuwa wannan jiha ta Jigawa domin koyarda matasan jihar yadda ake hada sabbi da kuma gyaran wayar ta salula.

Gwamna Badaru ya kuma dukufa ka’in da na’in wajen gine-ginen rumfuna a wasu kasuwanni da cibiyoyin kasuwanci dake manyan biranen jihar samarda kyakkyawan yanayin kasuwanci.

Dangane manyan ‘yan Kasuwa kuwa, gwamna Badaru ya samarda kyakkyawan yanayi ga ‘yan kasuwa masu sha’awar zuba hannun jarinsu a jihar wadda yin hakan ya jawo hankulan manyan ‘yan kasuwa na Duniya tun daga kasar Sin zuwa wannan kasa domin kafa harkokin kasuwanci.

Haka kuma wannan yunkuri ya ja hankulan babban Dan kasuwannan wato Alhaji Aliko Dangote shugaban rukunin kamfanonin Dangote zuwa wannan jiha domin zuba jarinsa a fannonin noma da masana’antu.

Gwamna Badaru harwayau ya kuma jagoranci wani yunkuri na musamman yadda ya tabbatar da kafuwar wata cibiyar kasuwanci ta kasa da kasa tsakanin Nijeriya da makwabciyarta kasar Nijar.

 

A lokacin da yake kaddamar da wannan cibiya, gwamna Badaru ya ce cibiyar kasuwancin an kafa ta ne da hadin gwiwar jihohin Kano,Katsina,Jigawa da kuma jihar Zindar dake kasar Nijar ,wadda aka kafata a yankin garin Maigatari a jihar ta Jigawa.

Ya kuma ce, cibiyar zata taimaka matuka gaya wajen bunkasar kasuwanci a wannan yanki gamida bunkasar al’adun al’ummar dake wadannan yankuna baki daya.

Gwamna Badaru ya ce, tuni gwamnonin wadannan jihohi na Kano,Jigawa,Katsina da Zindar suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar wannan cibiyar kasuwanci tareda daukar alkawarin samarda duk kayayyakin da ake bukata domin bunkasar cibiyar.

Haka kuma gwamnan ya ce, gwamnatin jihar ta Jigawa yi zama na musamman da gwamnatin tarayya domin samun goyon baya wajen cimma wannan kuduri da ta sanya a gaba na bunkasa kasuwanci a wannan jiha.

Sannan gwamnan ya kuma ce, tuni wadannan gwamnatoci suka amince da gina titunan da suka ta shi daga Zinder-Magaria-Tinkim-Dungus zuwa Babura, da kuma titin da ya tashi daga Zinder – Matameye – Kongolom – Daura zuwa Kano sannan kuma da titin da ya tashi daga Zinder – Gidimuni – Washa – Dungas zuwa Maigatari duk domin tabbatar da bunkasar Kasuwanci a wannan yanki.

Shima da yake tofa albarkacin bakinsa a ya yin kaddamar da cibiyar kasuwancin gwamnan jihar Zinder Alhaji Musa Isa cewa ya yi wannan cibiya bayan bunkasa kasuwanci da zata yi,za kuma ta farfado da tsohuwar alakar dake tsakanin kasashen biyu na Nijer da Nijeriya.

Haka shi ma takwaransa na jihar Kano gwamna Abdullahi umar Ganduje ya lashi takobin bada gudummawar gwamnatin jihar Kano domin cimma kurin da aka sanya a gaba na bunkasa kasuwanci a wannan yanki.

Gwamnan na Jigawa harwayau, ya karbi tawagar wani kamfani na musamman mai zaman kansa mai suna Norwegian Company wadda suka lashi takobin kafa kamfanin samarda hasken lantarki mai amfani da hasken rana wadda zai samar da haske mai darajar megawat tamanin (80) a birnin Dutse.

Shugaban kamfanin ya bayyana cewa, sun amince da kafa wannan kamfani a Jigawa ne sakamakon yunkurin gwamna Badaru samarda kyakkyawan yanayin zaman lafiya da san bunkasar kasuwanci gamida albarkatun da Allah ya huwace jihar musamman hasken rana.

Ya ce kafin kammaluwar aikin, kamfanin ansu zai kashe zunzurutun kudi har kimanin naira milyan 150 kuma ana saran kammala aikin cikin karshen shekara mai kamawa ta 2017 domin cin moriyar shirin ga al’ummar Jigawa da sauran makwabtan jihohi baki daya.

Haka kuma ya kara da cewa, kamfanin tuni ya rattaba hannu kan yarjejeniyarsu da Gwamnatin Tarayya kan sayarwa da kamfanoni wani kaso na hasken da zarar an kammala aikin.

ire-iren wadannan ayyuka sune kadan daga cikin yunkurin gwamnan jihar ta Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru wajen ganin ya bunkasa harkokin kasuwanci a wannan jiha wadda tuni al’ummar jihar suka fara gamsuwa da cewa lallai wannan yunkuri ya fara haifarwa da jihar da mai ido.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: