Connect with us

TATTAUNAWA

Ba Abin Da Ya Kai Zaman Lafiya Dadi A Duniya —Sanata Matori

Published

on


SANATA SALISU IBRAHIM MATOCI tsohon dan majalisar tarayyar Nijeriya ne, a hirarsa da LEADERSHIP A YAU dangane da halin da Nijeriya ke ciki, Matoci ya nanata cewar babu wata manufa da za ta cimma gaci ba tare da zaman lafiya ba, ya kuma hori ‘yan Nijeriya da su zauna da juna lafiya domin bunkasa tattalin arzikin kasar ba tare da an kawo baraka ba. Ya kuma tabo wasu bangarorin na daban. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi:

A halin da muke ciki an bayyana cewar Nijeriya ta fita daga matsin tattalin arziki ko me zaka ce kan hakan?

Eh to daga dukkanin alamu haka din ne, sai dai kai ka san alkaluma irin wadanda akan bayar daga hukuma da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ba kasafai ainihin talakawa da su ke kauye da dazuka za ka fahimce shi kamar yadda mutanen birni za su fahimta ba. amma dai duka abubuwan da suka faru a Nijeriya ya zama dole a godewa wadanda suke tafiyar da al’amuran tattalin arzikin kasar, da irin yunkuri da kokarin da suka yi, domin kila da ba din irin yunkurin nasu ba da tabarbarewa da lalacewar al’amura da sun haka nan. Da yanzu ba ana maganar farfadowa bane, da an zo ana maganar ta ina za a gyara kenan. Kenan sai mu yi hamdala.

Duk da maganar nan taka, takawa ba su gani a kasa ba. ko kana da wani abin da za ka ce garesu domin su kwantar da hankulansu don ganin an cimma nasara?

Abin da zan fada wa ‘yan Nijeriya shi ne abin da aka saba fada musu kullum ni ma ina fada. Muna dai fatan Allah ya sa canji din nan da mu ka yi ta ambatonsa tun daga shekaru 2 zuwa 3 da suka wuce ya zama mana canji ne na alkairi, canji wanda jama’an kasa za su amfana su kuma ci moriyarsa. Muna fatan da mu da su kowa ya mori wannan canjin Allah kuma ya sa haka.

Ana samun ‘yan sabani da kuma rashin jituwa a tsakanin wasu bangarori a Nijeriya me zaka iya cewa akan wannan?

A takaice dai bari na fada maka, duk abin da dan adam zai yi, ko yake nema ko yake da shi a duniya, babu abin da ya yi kusa-kusa da ya kai zaman lafiya. Zaman lafiyar nan da ka gan shi za a iya sayar da komai da aka mallaka domin a samu mallakar zaman lafiya. Matukar babu zaman lafiya to tabbas an rasa komai, idan kuma akwai zaman lafiya to ana da komai. A don haka duk wani mutum kirki a Nijeriya mai son kawo ci gaba wa al’ummansa da yankinsa, babu abin da ya kamace sa fiye da ya roki al’umman kasa da al’ummansa kan mu daure mu cije mu zauna lafiya da juna. Mu kuma sani cewa zaman lafiya duk yadda za a yi, in har da yadda za a yi din to a tabbatar da an same shi, shi ne mafi alkairi. Ba wai ta hanyar tashin hankali ba.

Domin shi zaman lafiya ba za ka taba iya kwatantashi akan kowanne irin sikeli ba; sai lokacin da ka rasa shi ne kuma za ka fahimci muhimmancinsa. Sannan duk abin da ba a yi shi a teburin shawara ba to…. sai zaman teburi ya gagara ake tafiya fagen yaki, kuma mafi akasarin lokaci shi yaki baya karewa sai an koma teburin shawarar nan. In dai dole a teburin shawara za a fara, kuma a nan za a kare to me zai sanya ma tun farko a bar teburin shawarar nan? Sabili da haka duk wata matsala da ta kunno kai yana da kyau a samu masu hankalin ciki, masu lafiyayyen hankali su zauna su dubi gaba dai, da me ke faruwa a duniyar tarihi da kuma me ke faruwa a yanzu su fitar da mafita. Yanzu idan ka dubi kasashe irin su Libiya, Irak, Yemen, a baya-bayan nan kuma irin su Katar ka duba irin dumbin arzikin da Allah ya yi wa Katar, sannan mutane ne wadanda dukkaninsu ba su wuce mutane miliyan biyu ba, amma a kowace rana wayewar garin Allah sukan samu abin da ya kai dala miliyan 100, duk adadin mutanen kasarsu miliyan 2 ne. ya kamata mu gane cewar babu abin da ya fi zaman lafiya, duk kokarin da zamu yi, duk kuma hankoron da zamu yi a Nijeriya, muke duba ya ya kasashen da suke tashin hankali suke wanyewa. Yanzu kasashen da na jero maka a sama, idan kana kallon telabijin da labarai na jarida ko kana shiga wasu kafafen watsa labarai za ka ga yadda mutane suke tururuwar shiga jiragen ruwa, wasu kuma a kafa, wasu a mota, suna kokarin su tsere daga muhallansu na haihuwa sune neman ketare teku, su bar kasarsu na asali, kasarsu da aka sansu. Yawancin wadanda suke wannan gudun kuma fa, ba wai zauna gari banza bane, daga Likitoci, Injiniyoyi, masu arzikin gari, ‘yan kasuwa, ma’aikata, da masu ilimi sannan ga manyan malamai da farfesoshi su ne suke wannan gudun suna barin matayensu da ’ya’yansu. Mata ba ta san inda mijinta ya ke ba; miji bai san inda matarsa take ba. daya bai san inda uwarsa take ba kowa ya ba-zama neman mafita da ceton ransa. Kowa na kokarin ya ketare teku don kauce wa bala’in da ke faruwa a kasarsa. Don Allah ina amfanin haka? Ina riba a cikin rikicin? Mutane ne wadanda a lokacin da suke gidansu suna cikin bushasha suna cikin jin dadin rayuwa, yau sun zama suna tafiya har mutum ya iya najasa a jikinsa ma bai sani ba sabili da dimauta da kuma firgita.

Wani karin bala’i da tashin hankali ma, su kansu turawan nan su ba da alkaluma kan cewa kowani mutum dubu idan suka hau kan jirgin ruwan mutum dari uku ne kadai suke samu su tsira. Dari bakwai din nan wasu kifaye sun cinye, wasu dabbobin ruwa ma haka, wani kuma ya fada ruwa ya mutu. Don Allah ‘yan Nijeriya ba zamu dauki darasi daga irin wadannan kasashen mu zauna da juna lafiya ba?. duk mai neman kawo hargitsi da sunan yanki abin da ke neman jawo wa Nijeriya kenan ba maslaha ba.

Nan da wasu ’yan watanni za a fara kada gangar siyasa a Nijeriya kana da shawarori ga masu neman tsayawa takara da ‘yan bangan siyasa?

Shawarar nan dai dukka magana daya ce, abin da ya kamata ’yan siyasarmu su gane shi ne musamman ma matasanmu, su gane duk wanda ya shiga cikin siyasa daman sunan abin aka ce zabe. Daman za ka shiga zabe ne saboda abu biyu, nasara ko akasinsa. Ita faduwa na siyasa koda an ce ka fadi baka fadi ba, domin kai ma kana nan, kana kuma daga cikin wani bangare na tafiya, sai dai in kuma ka ki a bisa zabin kanka. Domin dukkanin akida mun sani shi ne wanda za a bi domin kyautata kasa a kowace jam’iyya kuwa mutum ya ke. Idan kai Allah ya sa ka ci shugabancin a wani sashi, kada ka iya tunkaho ka nuna wa jama’a su ba su iya ba; har ma ka yi kokarin yin sabo, ka nuna shi ma Allah din da ya baka, kamar kawai a dole ne ya baka, wanda kuma ba a yi wa Allah dole ko tilas. Amma idan ka tafi da imani a ranka ka tafi da wadanda ka kayar da su, ka jawo su a jiki kuka tafi tare domin gina kasa sai ka ga mulkinka ya yi albarka kowa yana maka addu’ar kammalawa lafiya. Sabanin hakan kuma ba sai an fada maka ba. sannan shawarata ga duk wani dan takarar da ya nemi wata mukami ya fadi, idan ka fadi to ka yarda cewar haka Allah ya shirya  kuma shi ne mai iko a kan komai. Fiye da shekaru 30 shugaban kasar da ke ci yanzu Muhammadu Buhari ya ke neman shugabancin Nijeriya ya na fadi, ya fadi da bai fadi ba, an ce ya fadi shekaru 30 yana gwagwarmaya amma yanzu ba ga shi ya samu nasara ba. duk lokacin da Allah ya ba ma wani sai ka masa addu’a kai kuma ka jira lokacinka. Matasa a daina sanya ku fada da juna da sunan siyasa

Kasantuwarka tsohon dan siyasa, akwai matsalar nan da ke faruwa yanzu a cikin siyasar Nijeriya, inda za ka ga ’ya’yan jam’iyya daya ne ke fada a tsakaninsu a maimakon fada da jami’iyyun adawa kamar inda aka saba a shekarun baya, mene ne ka ke gani ya jawo hakan?

Hadama ita ce ke jawo wannan, hadama ita ce babbar illah, ita ce musifa, ita ce fitina. Kusan kashi 70 na cikin bala’o’in da muke fuskanta ita ce ke haddawa wato Hadama. Kowa yana kokari yana himmar cika jakarsa, koda halas ko haram shi dai kawai ya cika jakarsa makil. Mafiya yawa ban ce dukkan ‘yan siyasa ba, wannan ita ce matsalar, kowani dan siyasa cika jakarsa ne a gabansa, jakar da ba za ta taba cika ba kuwa, cikar jaka ita ce ka zama mai godiyar Allah mai wadatar zuci. Mai gamsuwa da abin da ya samu shi ne riba.

Mece ce fatarka a karshe?

Fatana Allah ya zaunar da kasarmu lafiya, matasanmu da suke gararanba a kan tituna su gane cewa sune shuwagabanin gobe, idan suka lalata kawuwansu da shaye-shaye da fadace-fadace to suna cutarka kansu, suna kuma cutar kasa ne domin nan gaba za a ga illar hakan. Ina fatan matasan mu su zama na kwarai sosai. Domin sune fatanmu nan gaba. Allah kuma ya yi mana jagoranci.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI