Connect with us

KASUWANCI

Babu Wata Hanya Da Zata Bunkasa Kasuwancin Dan Adam Fiye Da Ilimi —Umar Mijinyawa

Published

on

Daga Mustapha Ibrahim Kano

An bayyana cewa babu wata hanya da dan Adam zai samu cigaba a dukkan harkokin da yasa gaba fiye da a ce mutum ya samu ilimi na zamani da kuma na addini.

Wannan bayyani ya fito ne daga bakin Manajin Darakta na kamfanin ‘Sahad Stores’ na kasa, Alhaji Umaru Adamu Mijinyawa a bayan kammala wata gagarumar walimar cin abinci da kamfanin ya shiryawa‘yan uwa, abokan hulda, da wasu malaman addinin Musulunci da ke Kano, a dakin taro na ‘Marha Ebent Center’ da ke unguwar ‘Farm Center ‘ Kano a karshen makon da ya gabata.

Mijinyawa ya shawarci matasa kan su jajirce wurin neman ilimin addini da na zamani, musamman ilimin kwamfuta da kasuwanci, saboda wannan ilimi na da muhimmanci a cigaban zamani da hulda ta kowanne fanni.

Haka kuma yayi kira ga hukumomi akan samun dawwamammen hasken wutar lantarki mai karfi ta yadda kamfanoni da masana`antu zasu samukarfin sarrafa kayayyaki yadda dubban matasa zasu samu aikin yi a ko ina cikin kasar nan.

Shima a karshe a Jawabinsa, Alhaji Kamal Adamu ya yabawa mahalarta wannan tarotare da yin farin ciki dangane da yadda abokan huldarsu, yan`uwa da abokan arziki suka amsa kira a wannan muhimmiyar rana ta farin ciki.Sannan ya yabawa Sheikh Yakubu Tudun Wada da kuma Mallam Saminu  Abdulkadir Yakasai akan Nasihohin da suka gabatar akan hukunce-hukuncen zamantakewa na yau da kullum a tsakanin al`umma magidanta da iyalensu da sauran fannoni na rayuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!