Connect with us

KASUWANCI

Gidauniyar HOME Ta Koka Kan Shigo Da Gurbatacciyar Masara Nijeriya

Published

on

Daga Abubakar Abba

Gidauniyar lafiya wacce aka kiranta turance( Health of Mother  Earth),ta koka a kan yadda ake shogo da masara mai dauke  da sinadari cikin kasar nan da aka kiyasta kudinta ya kai Dalar Amurka miliyan tara.

Koken na kunshe ne a  wata takarda da gidauniyar ta bai wa jaridar LEADERSHIP A Yau wacce kuma ta samu sa hannun wani jami’in ta Joyce Ebebinwe.

Sanarwar ta ce, “mun karanta wani rahoto da na taron manema labarai da Darakta Janar na Hukumar sanadarai na kasa inda ya yi koke irin wannan masara da ake shigo da ita kasar nan.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, rahoton a baya ya bayyana cewa, wani kamfani mai suna Diamond, ya shigo da masarar ta hanyar jirgin ruwa da ke jihar Legas da aka kiyasta kudinta miliyan 144.29 na Dalar Amurka.

Bayan kwana biyu kuma, sanarwar ta kara da cewa, wani kamfani mai suna Zola berthed shima ya shigo da masara da aka kiyasta kudinta ya kai Dalar Amurka miliyan shida da digo daya.

Sanarwar ta yi kira ga hukumar kwastam da ta sanya ido a kan shigo da wannan masara da ake shigowa da ita kasar nan.

Gidauniyar ta kuma gudanar da bincike a kasuwanni don wayar wa jama’a kai a kan wannan masarar.

Ta kuma yi amannar cewar manoman kasar nan za su iya wadatar da kasar nan da  abincin da ake bukata in an ba su taimakon da ya kamata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!