Connect with us

KASUWANCI

Kamfanin Takin Zamanin Jihar Kano Ya Samu Ribar Naira Miliyan 200

Published

on

Daga Mahmoud Yakubu

Kamfanin takin zamani mallakar gwamnatin jihar Kano ya bayyana cewa ya samu ribar naira miliyan dari biyu bayan ya sayar wa da jihohi makwabtanta.

Da suke yi wa gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje bayani game da nasarorin, sun ce, kamfanin a yanzu, ba wai kawai yana sarrafa taki don amfanin jihar ba ne kawai, jihohin da Kebbi da Jigawa daKatsina da Niger duka suna sayen taken.

Hukumar kamfanin ta bayyana cewa, tana da kimanin taki na naira miliyan dari shida, kuma a yanzu, tana kan shirye-shiryen sarrafa taki na kusan naira miliyan dari biyar.

Gwamnan ya kuma  kaddamar da sababbin motocin aiki hudu da kamfanin ya siya tare da tirela guda biyu da za su iya daukar taki mai nauyin tan arba’in da Bas da a-kori-kura da aka saya a kan naira miliyan arba’in.

Gwamnan ya kuma sanar cewa, kamfanin ya gyara wasu na’urori a kan kudi naira miliyan dari uku da gwamnatin ta  ranto a shekarar 2015.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa, ta tuna da kamfanin ne, bayan shekaru da ya shafe, yana mace, inda a yanzu yake bada kyakkwan sakamako ta hanyar tarawa jihar kudin shiga.

Ganduje ya kuma nuna jindadinsa, gann yadda kamfanin yake yin amfani da damar yarjejeniyar da Nijeriya ta kulla da kasar Morocco na samar da takin zamani don kara samar da takin.

Tunda farko a jawabinsa, Babban Darakatan kamfanin, Bala Muhammad ya bayyana cewa, a yanzu hukumar kamfanin, tana yin gwaji a kan kamfanin, baya ga sayen sababbin motocin.

Bala ya ce, kamfanin ya kuma yi wa wasu motocin kwaskwarima.

Ya ce, an kuma yi wa dakunan ajiya na kamfanin da suke a waje-waje na jihar da aka yi watsi da shi kwaskwarima.

Daga karshe ya ce,  yanzu kamfanin na samar da taki kai tsaye ga kananan manoma ba tare da wata wahala ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!