Connect with us

KASUWANCI

Wasu Bankuna Sun Samu Ribar Sama Da Naira Bilyan 59 Ta Hanyar e-transaction

Published

on

Daga Sabo Ahmad.

A farkon wata shida na wannan shekarar ne wasu bankuna guda tara suka samu ribar naira biliyan 59.596, ta hanyar shiga da fitar kudi na zamani watau “e-taransactin” duk da cewa ana cire musu kudi sakamakon huldar da abokan huldarsu ke yi da wasu bankuna.

Bankin United Bank for Africa da Stanbic IBTC da Access Bank da Guaranty Trust Bank da Zenith Bank da FBN Holdings da Diamond da kuma Fidelity Banks said a suka samu ribar naira biliyan 34.849 , koda yake ya yi kasa da abin da suka samu a bara, inda suka samu ribar naira biliyan  76.155.

Ganin yadda Zenith Bank ya samu riba, sai wadansu bankuna suka sa raid a samun irin wannan riba, amma sai hakan ba ta samu ba. Sannan kuma bankunansuka dada samun raguwar riba ta asusun ajiyar abokan huldarsu.

A wata shida na farkon wannan shekarar ne, wadansu bankuna guda takwas suka samu ribar naira biliyan 24.747, wanda idan aka kwatanta da ta bara watau, naira biyan 28.368 za a gat a ragu. A cikin bankunan Zenith Bank ya ci gaba da rike kambinsa na ribar da yake samu, inda Bankin UBA ya zama zakara duk da raguwar ribar da ake samu ta hanyar e-transaction.

Tunda farko dai Babban Bankin Nijeriya, ya sake duba tsarin kudaden da bankuna ke cire wa daga asusun abokan huldarsu masu amfani da e-transaction inda ta rage yawansu.

A sake duba tsarin da Babban Banki ya yi  Aped Bank ya rage kudin yake caza ga abokan huldarsa ta intanet  daga naira 100 zuwa naira 50. Sai dai Bankin ya kara kudin kula da katin ATM daga naira 100 zuwa naira 600 a duk shekara.

Bankin UBA wanda ya samu gagarumar riba ta kashi 45.9 daga cikin dari, ya sauko daga naira biliyan 18.085  in aka kwatanta da bara wanda yake naira bilyan 19.781. Sai  GTB  wanda yake da kashi 61.4 daga cin dari ya sauko daga  naira biliyan 17.263 da ya samu a bara. Sai  UBA da yake biye da ribar naira bilyan 6.668.

FBN Holdings shima ya sauka daga naira biliyan 10.59 wanda ya samu bara zuwa naira bilyan 6.53, shi kuwa  Zenith Bank ya samu kashi 168 daga cikin dari kimanin naira bilyan 5.386 sabanin naira biliyan 2.008 wanda ya samu bara.

Zenith Bank  kuma ya sake naira biliyan 8.32 billion in aka kwatanta da bara da ya samu naira biliyan 8.92. Sai GTB  wanda ya samu karuwa daga naira biliyan 3.89 zuwa naira biliyan N4.87.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: