Connect with us

RAHOTANNI

Cibiyar Medicaid Za Ta Gudanar Da Taronta Na Shekara

Published

on


Kamar yadda cibiyar nan ta Medicaid wacce aka fi sani da ‘Medicaid Cancer Foundation’ ta saba gudanar da taro a kowacce shekara, domin samar da hanyoyin dakile yaduwar cutar Kansa, a wannan shekarar ta 2017 ma cibiyar za ta gudanar da taron wanda ta yiwa take da ‘A kore cutar Kansa’.

A jawabin shugabar cibiyar ga manema labarai, Uwargidan gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Bagudu Shinkafi ta bayyana cewa taron na wannan shekarar za a gudanar da shi ne a watan Oktoba a Jihar Kebbi da babban birnin tarayya Abuja.

Ta kara da cewa taron na wannan shekarar zai zo da wani salon a yin tattaki domin wayarwa da jama’a kai da safe, sannan kuma za a shirya wasannin kwallo da yamma, wanda za a gayyato manyan ‘yan kwallo da kuma shahararrun ‘yan wasa.

“Cibiyar MCF na aiki tukuru tare da kamfanonin maganunguna domin ta iya rage tsadar iya yin maganin Kansa, wanda ba karamin wahalar da iyaye da ma’aikatan kiwon lafiya hakan ke yi a Nijeriya ba. Mun cimma wannan nasarar ta hanyar samun tallafi da kuma shirya taruka na musamman.” In ji shugabar cibiyar.

Jawabin ya jaddada cewa taron na wannan shekarar zai kasance na yin tattakin mutum miliyan daya a Birnin Kebbi a ranar 10 ga watan Oktoban 2017, inda kuma za a buga was an kwallon kafan a ranar 21 ga watan Oktoban 2017.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI