Connect with us

LABARAI

Kasar Faransa Ta Musanta Zargin Nijeriya Akan IPOB

Published

on


Ofishin Jakadancin kasar Faransa da yake Nijeriya ya musanta zargin da gwamnatin Nijeriya ta yi a jiya na cewa Hedikwatar kungiyar tsagerun ‘yan IPOB a kasar Faransa take, a takardar da Mista Claude Abily babban mai ba da shawarwari a kan harkokin siyasa na ofishin jakadancin Faransan ya ba manema labarai a safiyar yau alhamis, yace, ‘lallai mun damu da batun da ministan yada labarai, Mista Lai Muhammad ya yi, na cewa a kasar Faransa hedikwatar samar da kudade na tsagerun IPOB take.’

Abily yace, ‘a shirye kasar Faransa ta ke wajen bada hadin kai ga gwamnatin Nijeriya a tantance gaskiyar batun, kasar Faransa ta dade ta na baiwa Nijeriya taimako akan yakin da take yi da rashin tsaro, mu ba mu da wata masaniya akan wannan batun’.

‘Muna kara jaddada goyon bayan mu ga gwamnatin Nijeriya akan duk matakan da take dauka domin samar da tsaro a kasar.’ Inji Abily

Jiya Laraba ne dai ministan yada Labarai na Njieriya Lai Muhammad yace gwamnatin Nijeriya ta san ina ne asalin inda kudade suke shigowa tsagerun IPOB daga kasashen waje daban-daban, kuma za mu yi kokarin dakile wannan kafa ta samun kudin tsagerun.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI