Connect with us

WASANNI

Dole Sai Luke Shaw Ya Sake Dagewa — Mourinho

Published

on


Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Luke Shaw, dan asalin kasar ingila ya na bukatar ya sake dagewa idan har ya na son ya cigaba da buga wasa a kulob din.

Mourinho ya yiwa dan wasan wannan gargadi ne lokacin hirarsa da manema labarai a shirye-shiryen da ya ke na fafatawa da kungiyar Southampton a wasan Firimiya sati na shida a filin wasa na ST Mary’s da ke kasar Ingila.

Kociyan ya ce, dan wasan ya dade ba ya wasa sakamakon jiyya da ya yi, saboda ciwo, kuma kungiyar yanzu ta na cikin yanayi mai kyau, saboda haka ya na bukatar ya sake dagewa don ganin ya yi daidai da ragowar ’yan wasan kungiyar.

Mourinho ya kara da cewa, akwai ’yan wasan da a wasu kungiyoyin har yanzu ba su fara buga wasa ba, kuma ya na jin masu koyar da su su na cewa ’yan wasan ba su shirya ba ne, saboda haka shi ma idan ya ce Shaw bai shirya ba, ba abin mamaki ba ne.

Ya ce, dan wasan ya na bukatar ya mayar da hankali sosai idan har ya na son ya dawo buga wasa a cikin ’yan wasa na sha dayan farko a kungiyar.

Luke Shaw dai ya yi fama da ciwo a shekarun baya inda har karaya biyu ya yi a kafarsa tun daga 2014 a lokacin tsohon koci Luis Ban Gaal ke kubgiyar.

A yanzu dan wasan ya dawo, inda ya buga wasan da kungiyar ta doke kungiyar Burton da ci 4-1 a kofin Capital Cup ranar Laraba.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI