Connect with us

LABARAI

2019: Dankwambo Ne Magajin Buhari -Yakubu Da’u

Published

on


Wani Matashin dan Siyasa a jihar Gombe kuma mai kishin ci gaban Arewacin Nijeriya Alhaji Yakubu Da’u (Babawo), ya nuna cewa a zaben shekara ta 2019 Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ne ya fi dace wa ya zama shugaban Nijeriya.

Alhaji Yakubu Da’u, ya bayyana hakan ne lokacin zantarwarsa da Jaridar Leadership A Yau, inda yake cewa, duk cikin ‘yan takarar shugabancin Nijeriya da suka fito suka nuna sha’awar su ta yin takara ba wanda ya cancanta kamar gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo.

Ya ce, dalilinsa na bayyana hakan shi ne saboda duk shugabanin kasashen da aka yi a Nijeriya babu dan Arewa maso-gabas. Tunda Nijeriyar ana yin mulkin kama kama ne ma’ana can su taba can ma su taba, to yanzu Arewa maso gabas ne ta dace da shugaban kasa kuma Dankwambo shi ya fi cancanta.

Alhaji Yakubu, ya kara da cewa duk jam’iyyun siyasar da ake da su manyan su ne APC da PDP idan dai ci gaban kasa ake so a ajiye bambancin jam’iyya a yi cancanta don shi kadai ne wanda idan ya zama shugaban kasa zai magance matsalar Arewa maso-gabas da ta jima tana ciwa ‘yan

yankin tuwo a kwarya sannan ya daidaita wa kasar sahu.

A cikin zantawar ta mu ya kuma ce babbar matsalar Nijeriya ita ce samun shugaba mai kishi mai kuma mai jini a jika wanda yake da juriya don shi ne zai iya jajirce wa don ya ceto kasar sannan kuma Dankwambo zai iya kawo karshen duk wani tashin-tashina da ke faruwa a kudu da Arewa da ko’ina a wannan Nijeriyar ta mu.

Daga nan sai Alhaji Yakubu Da’u, ya jawo hankalin al’ummar Nijeriya musamman ‘yan arewa da cewa duk wannan fitintinu da suke faru wa a kasar nan da a yi hakuri a zauna lafiya da juna. Allah da ya hada mu waje daya ai bai yi kuskure ba, don me wasu tsiraru za su dinga kunna wutar rikici suna neman sai an raba kasa.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI