Connect with us

KASASHEN WAJE

Iran Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami

Published

on


Kasar Iran ta yi gwajin wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango, duk da cewa  Amurka na ta jan kunnenta da cewa muddin ta sami hujja yarjejeniyar da aka kulla da ita zai sukurkuce.

Tashan Talabijin na kasar ya sanar da cewa gwajin na makamin mai suna Khoramshahr an yi nasara, yayin wani  fareti na Soja a birnin Tehran.

Makamin wanda ke dauke da bidiyo a cikin sa na  iya tafiya mai nisan kilomita 2,000.

Ministan Tsaro na kasar ta Iran Amir Hatami ya bayyana cewa muddin wasu na maganganu dake barazana dole a kara karfafa harkan tsaron kasa, kuma babu yadda kasar za ta jira wani izini kafin yin duk wani makami da take so.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI