Connect with us

MAKALAR YAU

Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1439: Bukatar Hijira Bayan Hijira

Published

on


               Aliyu Dahiru Aliyu             [email protected]

Rubutuna a yau zai fara da tambaya ga ’yan’uwanmu Musulmi da suke murnar shiga sabuwar shekarar hijirar 1439. Tambayoyi ne da koda na yi niyyar ba da wasu amsoshin game da su amma ina burin kowanne daga cikinmu ya zauna guri guda domin ya amsa su da gaskiya a cikin zuciyarsa a lokacin da yake jin cewa tabbas babu wanda yake karanta zuciyarsa sai Ubangijinsa. Ba na bukatar amsar ta kasance ta hanyar Musuluncin siyasa wato Islamus Siyasiy, kamar yadda Abbas Al’akkad yake kiransa, ko kuma Musuluncin bangarencin gari wato Islamul geography kamar yadda Shukaib Arsalan yake kiransa. Musuluncin siyasa ya yi nisa ga tsari da ruhin da aka kafa addinin Musulunci a kansa.

Musuluncin siyasa, kamar yadda muke ganinsa a yanzu, ya yi wa addinin illa fiye da yadda ya amfana daga gare shi. Musulunci ne da mabiyansa suke bauta wa jagorori da manufofin wasu kasashe maimakon su bautawa Ubangijin addininsu. Abin takaicin ne ya kasance agun wasu daga mabiya Musulunci duka abin da kasar Saudiyya da jagororinta suka dabbaka to suna ganinsa a addini! A gunsa duk abin da ya faru da Musulunci na lalacewa ko tashin hankali to laifin Iran da ’yan Shi’a ne.

A kwanakinnan a kafar sada zumunta ta Facebook nake ganin wani ya takarkare yana kare duka muradun Saudiyya da sunan addini. Daga siyasarta har zuwa alakarta da kasashen waje, kai har rigimar Amurika da Koriya ta Arewa sai da ya shigo da maganar addini a ciki! Har a gidan rediyo na saurari wani babban malami, abin takaici kwarai, yana yin iya karfinsa wajen kare siyasar Saudiyya da kuma dora laifin duk abin da yake samun Musulmi na matsala a kan Iran. Lokacin da akai turmutsutsu a hajjin bara, shi ma haka na ji shi ko kunya bai ji ba yana cewa laifin Iran ne. Suma agun daya bangaren ba ta canja zani ba. Duk matsalar da take samun Musulmi to suna ganin laifin Saudiyya ne. Shin ba zai zamo abin takaici ba, a ce hatta fadowar karfen ginin da aka yi a shekarar 2015 a cikin harami, wanda iska ce ta kado karfen aka samu hadarin, sai da wasu suka ce laifin Saudi Arabia ne da take burin kashe Musulmi ba? Yaushe za mu hankalta don mu gano cewar siyasar Gabas ta tsakiya mafi yawanta ba rigimar addini ba ce? Yaushe za mu gane rige-rigen shugabancin Gabas ta tsakiya ne tsakanin Saudiyya da Iran ake lullube shi da sunan Shi’a ko Sunnah?

Shekara 1439 bayan Annabin Rahama (saw) ya taso daga garinsa na Makka zuwa garin Yathrib da ake kira Madina a yanzu. Me za mu koya acikin wannan tafiyar a wannan lokacin da muke cikin rauni? Me za mu fahimta na daga abin da ya buya daga falsafar da take kunshe da tafiyar? Me za mu gane a lokacin da muka watsar da iliman masu ilimi a cikin addinin? Akwai bukatar mu nutsu mu fahimta don mu gane abin da za mu koya a rayuwar Manzon Allah a zamanin da Musulmi muke cikin duhu. Ilimin da aka samu daga zamanin Alfarabi da Ikhawanus Safa a falsafa,

Muhammad bn Zakariyya Razi da Ibn Sina a Magani, Ibnul Haitham da Alkhawarizmy a Kimiyya da Lissafi, Gazhali, Fakhr Arrazi, Ibn Rushd da sauransu da yawa a yanzu duka sai dai labari kawai. Hatta ilimansu ba ma karantawa balle mu fahimci sakon addinin. Mun watsar da komai mun koma rigimar siyasar addini yayin da Turawa suka debe ilimin suka bar mu muna yi musu biyayya. René Descartes, babban masanin falsafar nan na Turawa, an tabbatar ya debi iliman Abu Hamidil Gazzhali a falsafa musamman bangaren ilimin Metaphysics. Ibn Khaldun kuwa da Arnold J Toynbee  yake cewa bai taba ganin kamarsa ba a tsawon tarihi,ba mu damu da karanta babban littafinsa wato Mukaddima da ya zuba ilimi a cikinta ba. Daga Galileo Galilee zuwa Albert Einstein, dukansu sun yi amfani da ilimin Alhazen wajen kawo cigaban da sukai a Kimiyya. Amma mu me muke a yanzu? Me muka fahimta da za mu fahimtar da wasu game da addinin? Irinsu Sayyed Hussein Nasr, Ali A Mazrui, Ahmed Zewail, Prof. Abdus Salam, Hamza Yusuf ko Shahid Mutahhari ’yan kadan ne a duniyar Musulmi a yau.

Rayuwar Manzon Allah (saw) da duk abin da ya aikata ya fi iya abin da muke kallo kawai. Duk da a guraren taron addini an fi gaya mana bashariyyar Manzon Allah (saw), amma shi yana so mu koyi Insaniyya irin tasa ne. Mafi yawa an fi gaya mana ya gashin Manzon Allah yake, Ya tsawon girarsa take, ya yanayin tafiyarsa take, ta ina ya bi da zai yi hijira ko kuma me akai a hanyar hijirar. Duk da muna bukatar sanin tarihin da siffofin amma ba wannan ne mafi muhimmanci ba. Waye a cikinmu aka ce ya gyara girarsa ta koma irin ta Annabi? Wa aka ce ya ya yi tafiya irin ta Annabi? Wa aka ce ya yi dariya irin ta Annabi? Dukanmu babu wanda zai iya domin wannan bashariyya ce da ta kebe Annabi kawai shi kadai. Amma Insaniyya ita aka umarce mu mu kwaikwaya. Daga yadda Manzon Allah yake tausayin talaka zuwa yadda yake girmama iyalinsa. Daga yadda yake mutunta sahabbansa zuwa yadda yake kyautatawa makobtansa. To me za mu koya daga hijirarsa? Me zuciyarmu za ta kwankwada daga ruhin wannan hijira a lokacin da take cika shekara ta 1439?

Wannan lokaci ne da za mu yi hijira daga duhun jahilici zuwa neman ilimi. Lokaci ne da za mu yi hijira daga tashin hankalin da yake samunmu a kasashen Musulmi, tun daga Afghanistan zuwa Syria, daga Somalia zuwa Nijeriya, zuwa cikakken zaman lafiya. Lokaci ne da za mu  yi hijira daga Musulincin siyasa zuwa Musulincin Ubangijin da babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi kadai. Abin da ya kamata mu tambayi kanmu a kodayaushe (ba lallai sai shekara ba), ina muka dosa? Ina rayuwarmu take nufa? Ina halayyar al’ummarmu take nufa? Me muke don mu canja kawunanmu? Me muke aikatawa don taimakon al’ummarmu? Me muke don wanzuwar zaman lafiya da isar da sakon rahama a duniya? Mutane kala biyu ne, kamar yadda Aliyu bn Abi Talib yake fada, ko dai dan uwanka a addini ko kuma dan uwanka a mutuntaka. Mu yi aiki don cigaban al’umma dukanta ba don cigabanmu mu kadai ba. Wannan ita ce babbar hijirar da za mu yi don tunawa da waccan hijirar ba wai murna kawai ba.

Akwai banbanci tsakanin abubuwa a yadda suke (noumena) da kuma abubuwa a yadda muke daukar su (phenomena). Misali (a Kimiyya): kowane abu da muke gani da kaloli, asalinsa baki ne, har sai idan haske ya haska abin sannan yake samun kalarsa amma babu abin da tun asalinsa da ma kore ne ko shudi ne ko rawaya ne. Dukan abubuwa masu kaloli asalinsu bakakene. Idan kaloli suka tattaru a kan abu to sai ya ba da fari. Wannan Physics da Basic Science ne da aka koya mana tun muna ’yan kanana da ina zaton duk dalibin kimiyya ya san haka. Tamkar haka ne a lissafin shekarar da muke yi. Shekarar watan sama (lunar calendar) suna ne kawai da yake nufin zagayen da wata yake yi a jikin duniya. Shekara ba ta nufin mun fita daga wani yanayi mun shiga wani yanayin bayan kwanaki 360 ko fiye ko kasa da haka. Wannan tunanin gama-garin jama’a ne wadanda ba su da ilimin Kimiyya ko Falsafa. Ba za mu taba samun ribar abin da muke ba har sai mun kawo canji da kanmu ba wai mu jira sabuwar shekara ta kawo mana canji ba. Wannan ita ce hijirar da muke bukata a yau bayan hijirar Manzon Allah (saw).


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI