Connect with us

RA'AYI

WALƘIYA: Yadda Mutum Ke Iya Samo Tallafi (1)

Published

on


tare da: Ibrahim Mohammed Aboki i-mel: [email protected]

Mako biyu da suka wuce mun yi tsokaci a kan irin kalubalen da ke gaban Arewacin Kasar nan, wanda kuma baya iya rabuwa da matsalar tattalin arziki, na karfafi matasanmu da su dage wajen nema wa kansu madogara, ba kuma lallai sai irin madogarar da suka so ba. A’a, duk wacce ta samu a yi amfani da ita. In an nemi wata ba ta samu ba, sai a canja da wata, da haka har a dace a watan. Mun raba ayyukan zuwa gida hudu: aikin albashi- wanda ya hada da na gwamnati da kungiyoyi da kamfanoni da kasuwanci da sana’oin hannu da kuma nomad a kiwo.

Dole mu yarda da yadda talauci ke taimaka wa wajen durkushewar wasu fitattun mutanen da in suka samu dama, al’umma za ta samu karu wa da ilimominsu matukar karuwa. To amma da yawansu ba sa samun damar. Kila dalilin ma kenan da ya sa aka samar da wasu tsaruka na tallafi ga irin wadannan mutanen, walau na gurbin yi ko karo karatu na gajere da dogon zango, da kuma tallafin jari don yi ko bunkasa kasuwanci.

Darasin yau a kan kasuwanci ne. Don haka zan haska wa masu karatunmu a kan hanyoyin da za su bi wajen samo wa jari domin fara wa ko bunkasa kasuwancin da suka kudurci yi ko suke yin sa.

Bincike ya tabbatar da cewa, daya daga cikin manyan matsalolin kasuwanci a kasashe masu tasowa shi ne rashi ko karancin jari. Hakan, kamar yadda binciken ya tabbatar, ya sa a cikin duk sabbin kasuwanci guda biyar, ‘daya ne tak yake kai wa ga cin nasara, hudu karye suke yi’. Dalilin Kenan da ya sa wasu kungiyoyi da hukumomi ko daidaikun mutane ke samar da tsaruka na zakulowa zakakuran mutane masu kyawawan fikirorin kasuwanci, sannan kuma ba su da jari ko kuma suke bukatar kari; sai su dora gasa wacce duk wanda ya yi nasarar samu, za a ba shi jari domin tabbatar da wannan fikira ta sa, ko kuma kara bunkasa ta. Akwai masu bayar da rance, akwai masu bayarwa kyauta da kuma masu hada duk biyun, ya danganta ga wanda mutum ya cika ko ya samu nasarar dace wa. Shi dan kasuwa ayyukan yake samarwa ba kamar ma’aikacin gwamnati ba- wanda shi aka samarwa aikin.

Takwarorinmu ‘yan kudu sun yi nisa a wannan harkar, da yawansu sun samu alheri mai yawa a ciki. Wasun su ma, sun mallaki har digiri na uku amma ba su taba sha’awar aikin gwamnati ba sun kuma samu abin da da yawan ma’aikatan gwamnati har su yi ritaya ba za su samu ba, a cikin ‘yan shekaru kadan. Da yake mu a nan Arewa ba mu waye sosai da wadannan ba, zan so yin magana ne a kan wadanda suke bayar da kyautar, kila daga baya in lokaci ya ba da dama mu yi magana a kan sauran.

Kafin na shiga cikin bayanin, yana da kyau mu gane cewa, kafin mutum ya tsunduma cikin wannan sana’a akwai bukatar ya samu komfiyuta mallakarsa, babbar waya ko duk biyun, da kuma tsarin yanar gizo (internet) da zai yi na amfani da su wajen bude abubuwa da cikasu cikin sauki. Zai iya yi a shagunan aikin kwamfyuta na ‘yan kasuwa, sai dai idan nasa ne, zai samu damar yin duk abin da yake son yi, walau cikin dare ko safiya ko duk lokacin da ya so ba tare da sai ya jira wani ko ya je wani waje ba.

Kusan dukkan abubuwan gasa na cike-cike sun zama a yanar gizo ne (online) a yau, don haka in da mutum zai rasa kwamfiyuta ko internet, to kuwa ya samu babbar nakasu a wannan layi. Ta yiwu wani ya ce to ai shi bai iya kwmfyuta ba, ko kuma ya samu horas wa a kanta amma bai iya ba. To sirrin shi ne ka mallake ta, da sannu za ka koya daidai da bukatar ayyukanka, a cikin lokaci kankani. Yawan amfaninka da ita yawan koyon ta da za ka yi.

Safukan yanar gizo masu tallata wadannan garabasar suna da yawa. Sun hada da: Opportunity desk for you (www.opportunitydeskforyou.org), Yali Network Face to Face (yalinetworkfacetoface.com), Utibe Etim (utibeetim.com). Sannan akwai gidauniyar Tony Elumelu, wani inyamiri wanda shi ne tshon shugaban bankin hadin gwiwa na Africa (UBA) a Nijeriya, ya kafa. Suna zabar mutum dubu daya duk shekara a nahiyar Afirka su basu jarin dala dubu biyar, wanda yake daidai da naira miliyan daya da dubu dari biyar da ashirin da biyar (1,525,000) a kowannensu. Akwai USADF na gwamnatin Amurka, Fire Africa na gamayyar wasu kungiyoyi, Big Portal na Bankin duniya da hadin gwiwar gwamnatin Nijeriya da sauransu.

Abu na gaba shi ne cancanta. Kowace irin gasa tana da cancanta (eligibility criteria). Idan na ce cancanta ina nufin wadansu sharudda da aka sa wadanda sai mutum ya cika su kafin ya shiga gasar, kuma gazawarsa a guda daya zai iya haramta masa shiga ko cin wannan gasar. Wadansu sukan hada da shekaru, wasu da jinsi, wasu da kasashe ko yanki, wasu da nau’in aiki ko kasuwanci, wasu da bangaren karatu ko kware wa da sauransu. Kana bukatar tun da farko, ka duba su ka kuma tabbatar ka cika sharuddan, in kuma ba ka cika ba to ka da ka wahalar da kanka. Kawai ka hakura.

Kada ka bata wa kanka lokaci a kan abin da ba ka cika sharuddansa ba. Saboda wadannan damammakin suna da yawan gaske, kullum fitar da sabbi ake yi, kuma in da za ka mayar da cika su shi ne sana’arka to kullum yadda ka ga fitar rana, haka za ka ga faduwarta, ba tare kuma da ka yi duk abubuwan da kake son yi ba. Don haka, kawai ka dauki wadanda ka cika sharuddansu ka cika.

Da yake muna magana ne a kan nemo tallafin kasuwanci, to akwai bukatar mutum ya zama yana da manhajin yin kasuwanci (business plan), wanda a duk wani gasar bayar da tallafin kasuwanci kyauta shi ake tura wa, kodayake kowace gasa da irin yadda suke tsara tambayoyinsu, amma dai duk ba sa wuce tambayoyi a kan manhajin kasuwancin (Business Plan). Manhajin, ya kamata ya tabo dukkan bangarorin kasuwar da ake so a yi ko ake yi wadanda suka hada da gundarin fikirar kasuwancin, abin da za a yi ko ake yi, masu saya da girman wajen da za a sayar din, da kishiyoyin kasuwancin da yadda aka musu zarra, matsaloli da maganinsu, kiyasin damamamakin da kasuwancin ke da su da kuma gaza wa da lissafin kudi na kasuwancin, talla da kuma hanyoyin da za a tallata da sauransu.

Mun ce gasa, ya kuma kamata masu karatu su fahimci me ake nufi da gasa, cikakkiyar fahimta, saboda masu neman suna da yawa, sun fi yawan mutanen da za a zaba nesa. A wasu lokutan wasu ma ba wai ci ne ba su yi ba, a’a yawan mutanen da suka cika ne zai hana su kai wa ga nasara. Duk wata dama da yake da ita, ya yi amfani da ita, ka da ya raina girmanta. Kada ya yi aikin lalaci, ko kuma ya zama ya tura ‘yan wasu layukan da ya yi su a ‘yan mintinu ba. Aiki zai yi tamkar ma rubuta littafi. Ka tuna idan har mai kasa kaya kullum a kasuwa zai sha wahala a kudaden da ba su taka kara sun karya ba, ina kuma ga kai da in ka dace za ka samu miliyoyi kudi a lokaci guda? Kai ne ka fi dace wa da yin duk wata dawainiya domin ganin ka dace. Kenan dole ga duk wanda ya sa kansa, ya zama ya ja damara, ya yi aiki mai inganci da kyawun da duk wanda ya karanta zai shaida ya san abin da yake magana a kansa, ba kame-kame ko dogon turanci ba. Ba bukatar gaggawa, kowace gasa ana ba ta lokaci kafin a rufe.

Bai kamata don ka cika abu ba ka samu ba, ka dakatar da cika wa ko ka karaya ba. Wasu lokutan hakan na nufin gazawarka a wadansu abubuwa ne- wadanda kuma ya kamata ka bincika domin gyarawa, sake nema ko gwada wa a gaba, yayin da a wasu lokutan hakan ke nufin yawan da aka yi a gasar.

Kana bukatar tuntubar wasu na gaba da kai a kan wannan abin da kake kokarin cika wa ko nema, ko kuma ka samu mai yi maka saiti (mentor) na dindin a wannan bangaren. Muna da karancinsu a Arewa, amma in ka bincika ba za ka rasa ba. Sannan ya zama ka sabarwa kanka amfani da bangaren ‘google’ a intanet- wanda yake dauke da miliyoyin bayanai, domin yin bincike a kan kowane irin abu da kake bukata na ilimi. Amfani da google zai taimaka wa mutum matuka gaya wajen binciko muhimman bayanai dangane da wannan kasuwancin da yake son yi ko yake yi, saboda a mafi yawan lokuta alkalan gasar gwanaye ne ko masana a kan wadannan abubuwan da kuke rubutu, cikin sauki za su iya gane ka sani ko ba ka sani ba.

A yi hankali da ‘yan damfara, wadanda kullum suke shigar burtu a yanar gizo domin damfarar mutane. Abin da duk ka ga ba ka san shi ba, to ka yi tambaya a kansa, a kuma kiyaye tura kudi ko bayar da bayanan sirruka na asusun ajiyar kudi a banki, musamman mabudin cire kudi (pin cord) na injin cire kudi (ATM).

Za mu ci gaba sati mako mai zuwa


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI