Connect with us

MANYAN LABARAI

Dino Melaye Ya Arce? Idan Ya San Wata Bai San Wata Ba, Cewar INEC

Published

on


Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

A ranar Talata Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ƙi amsar takardun yi ma sa kiranye a ofishinsa da ke majalisar dokoki ta ƙasa ta hanyar yin layar zana, sannan kuma ya umarci sakatariyar ofishinsa da kada ta sanya hannu a kan takardun kotun, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta bayyana ta na mai nuna cewa, idan ya san wata, ai bai san wata ba.

Mai shari’a Nnamdi Dimgba na babbar kotun Abuja ne ya umarci INEC da ta kai wa Melaye takardun kiranyen cikin makonni biyu da yanke hukunci da kotun ta yi na halasta cigaba da yiwa sanatan kiranye bayan ta yi watsi da ƙarar da ya shigar ta dakatar da kiranyen a ranar Alhamis da ta gabata.

Binciken wasu manema labarai ya nuna cewa, tun a ƙarshen mako a ke yin kulli-kurciya da sanatan, inda ya ke dojewa amsar takardun da ya ke ganin za su iya kai shi su baro.

Lauyan INEC, Barista Yunus Ustaz Usman, ya ce, sakatariyar sanatan ma ta ƙi amsar takardun hukumar daga hannun masinjan kotu, ta na mai cewa, sanatan bai ba ta umarnin ta amsa ba.

Bugu da ƙari, an yi zargin cewa, masu gadin gidan Dino sun hana masinjan shiga gidan, sannan kuma su ka ƙi yarda su akrɓi takardun tun a ranar Alhamis ɗin.

“Bisa wannan abinda ya faru, za mu shigar da ƙara kotu mu na neman ta ba mu dama mu isar das aƙon takardun ta wasu hanyoyin,” in lauyan, wanda ya ƙara da cewa, har da takardun umarnin kotun ma a cikin takardun da a kai wa sanatan.

To, saidai kuma a wani labarin , Sanata Melaye ya ce ya bayar da umarni ga lauyoyan da ya sake garzayawa wata kotun ya nemi ta dakatar da INEC, domin a cewarsa kwanaki 90 da kundin tsarin mulki ya ƙayyade na yin kiranye sun riga sun wuce tun ranar 23 ga Satumba.

To, amma a wancan hukunci da Alƙali Dimgba ya yanke ya yi ƙarin haske da cewa, shigar da ƙara kotu da a ka yi ya dakatar da cigaba da lissafin yawan kwanakin har zuwa lokacin da kotun ta yanke hukunci, inda sannan ne lissafin kwanakin zai cigaba da ɗorawa.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI