Connect with us

MANYAN LABARAI

Gwamna Yari Ya Kalubalanci Jami’an Tsaro Sace Mutane Ke Tsorata Masu Zuba Hannun Jari -Dangote

Published

on


Daga Sulaiman Bala Idris

Daga Hussaini Baba, Gusau

Ganin yadda harkar kai hare-hare da garkuwa da mutane ke neman dawowa danye a jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar Yari ya kalubalanci Jami’an tsaro wajen yadda suke gabatar da aikin su a fadin Jihar ta Zamfara, musamman ganin yadda Mahara suke cin karen su babu babbaka a ‘yan kwanakin nan a Jihar, duk da hubbasan da ya ce yana yi wajen magance wannan abu, inda ya nuna matukan takaicinsa, tare da dora alhakin hakan a jami’an tsaron.

Gwamnan ya bayyana haka ne ga ‘yan jarida jim kadan bayan kammala taron Majalisar zartarwar jihar, wanda ta kunshi Sarakuna da masu ruwa da Tsaki a harkar Tsaro, inda ya gana da manema labaran a jiya Talata.

Gwamnan ya bayyana cewa, babu wata matsala da Jami’an tsaron ke gabatar masa face ya magance masu ita kowace iri ce. “Kuma duk abin da suka bukata na kudi ko kayan aiki, ban taba rage ko sisin kwaba ba, face na ba su. Sannan ya zuwa yau na ba su motoci dari uku da saba’in (370),” in ji Gwamnan.

Saboda haka sai Gwamnan ya nuna matukar takaicinsa da cewa yau wadannan mahara, ba ma a daji ba, cikin gari suke shiga da rana karara kowa na ganinsu su ci karansu babu babbaka. Ya ce, kuma yanzu haka ana tsorata ‘yan sanda a karkara da cewa maharan za su kawo masu hari, yanzu haka suna neman bacewa daga garuruwan da aka ce babu Jami’an a gari.

Gwamna Yari ya kuma nuna takacinsa da yadda harin da aka kai ofishin Hukumar kiyaye hadurra ta garin Tsafe ya kasance, inda ya ce sakaci ne sosai. “Amincin da talaka ke da shi ga jami’an tsaro, yanzu abin ya yi rauni bisa la’akari da yadda jami’an tsaron ke rike harkar. Kullum maharan nan sai barazana suke yi wa al’ummar yankunan karkara, tare da sace fitattun mutane,” Gwamnan ya nuna takacinsa.

Gwamnan ya bayyana cewa bayan da aka cimma yarjejeniyar da aka tsayar a kwanakin baya, sai ya zama wasu ’yan tsagera daga cikin mabiya Buharin Daji suka ki amincewa da wannan yarjejeniya, suka karya yarjejeniyar, wanda wadannan fandararru na yaran Buharin Dajin ne ke kai wadannan hare-hare, inda ya bayyana cewa sasantawa ce babbar hanyar samun zaman lafiya.

“Mun gano cewa akwai wata ’yar rashin jituwa tsakanin Buharin Daji da yaransa tun lokacin da ya yarda da shirin zaman lafiya da gwamnati. Saboda haka muna kira ga al’ummar jihar Zamfara su hada kai da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro don kare rayuka da dukiyar jama’a,” in ji Gwamnan.

Don haka sai Gwamnan ya tabbatar da cewa “na dawo Jihar don daukar gagarumin mataki, kuma yanzu haka Abuja zan je don ganawa da Shugabannin tsaro don kawo karshen wadannan ’yan ta’adda. Ba za mu lamunci wannan ta’addancin ba.”

Saboda haka sai Gwamnan ya yi kira da cewa, “don haka nake kira ga al’umna da su taimaka mana, duk inda suka ji bullar wasu wadada ba a san ko su waye ba, a sanar da Sarakuna don daukar mataki.”

A wata sabuwa, Shugaban Rukunan Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi gargadi kan yadda ayyukan masu yin garkuwa da mutane ya ke hana masu zuba hannun jari zuba jari a kasar nan, haka kuwa ya mugun dakushe harkokin tattalin arziki musamman a fannin noma, dangote ya fadi haka ne a wajen babban taron baje koli na harkokin noma wanda kungiyar ‘yan kasuwar manoma da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka shirya.

Injiniya Mosul Ahmad, shi ne ya wakilci Dangote a wajen taron, inda ya bayyana matsalolin da suke kalubalantar masu zuba hannun jari a harkar noma a Nijeriya, ya koka da yadda matsalar garkuwa da mutane ta yawaita a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, wannan ya tilasta wa masu zuba hannun jari da suke da gonaki barin gonakin nasu saboda tsoron fadawa hannun masu garkuwa da mutanen.

Ya kara da cewa: “halin rashin tsaro a kasar nan yana matukar kawo cikas ga harkokin noma. Mafi yawan masu manyan gonaki da ke kan babbar hanyar sun watsar da gonakin na su saboda gudun kada a yi garkuwa da su, matsalolin rashin filaye su ma matsaloli ne da suke kawo cikas a fannin kasuwancin noma, wanda dokokin mallakar filaye ce ta jawo hakan, kuma lallai in gwamnati ba ta yi wa dokar kwaskarima ba, to za ta haifar da muguwar matsala a fannin kasuwancin noma da ma tattalin arzikin kasa gaba daya.”

Ya shawarci gwamnati da ta duba lamarin sosai da idon basira, sannan ta samar da manyan filayen noma na kasuwanci.

Ya kuma kara da zargin gwamnati da nuna halin ko in kula da rashin bayar da hadin kai ga masu sanya hannun jari a fannin noma.

A karshe ya ce; “Harkokin noma ba zasu ci gaba ba a kasar nan, har sai duk masu ruwa da tsaki daga ma’aikatun gwamnati sun hada hannu waje guda wajen bayar da gudummawa ga masu zuba hannun jari a fannin kasuwancin noman.”

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI