Connect with us

RAHOTANNI

PDM Ba Ta Yi Hadin Gwiwa Da Kowacce Jam’iyya Ba

Published

on


Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Shugaban jam’iyyar PDM na Jihar Neja, Kwamred Musa Adamu Nasko ya ce, a halin da gwamnatin Neja ke ciki alheri ne ga jam’iyyarsa a 2019. Domin yadda sauran jam’iyyu ke samun baraka kullum jam’iyyarsa tana kara samun baki ne masu sha’awar siyasa ta gaskiya.

Nasko ya ce, akwai rahotannin da ake yada cewar mun yi hadin gwiwa da sabuwar jam’iyyar Legacy, wannan ba gaskiya ba ne illa dai akwai bakin haure da suka shigo mu da karfi suna tunanin jam’iyyar na zaune kara zube ne muka maka su kotu wanda a halin yanzu in ma hadin gwiwa ne to su ne suka yi abinsu can.

“Ba yadda za a yi jam’iyyar da ke da turaku masu tauri ta nemi hadin kan jam’iyyar da ko rijista ba ta samu ba, muna zaune da gindinmu kuma jama’a na ci gaba da amsa kiran PDM. Yanzu haka mun himmantu wajen bude ofisoshin jam’iyya a sauran kananan hukumomin da ba mu bude ba, don haka PDM ta shirya wa 2019 idan Allah ya kai mu”, in ji Nasko

Dangane da maganar ‘yan kutse kuwa, Nasko ya ce, “Mun kai su kotu, kuma kotu ta dakatar da su yin wani abu da ya shafi PDM, don mu ne ‘yan jam’iyyar na asali kuma abin da muke yi a jam’iyya shi ake ce wa dimokuradiyya. Ba mu amince da yi wa kowane mamba rijista ba dole sai ka koma mazabarka ko da daga ina ka fito kuwa, kuma komai girmanka wannan ita ce dimokuradiyya”.

Tare da cewa, “Ina kiran magoya bayanmu da babbar murya da cewa kowa ya isa mallakar katin zabe da ya gaggauta zuwa cibiyar da ke da alhakin bada takin zabe ya mallaki nasa domin shi ne ‘yancin duk wani dan kasa nagari. Masu tunanin ci gaba da siyasar doki-dora da karfi su sani lokaci ya wuce yanzu zamani ne na kuri’arka ‘yancinka, mu yanzu a jam’iyyance mun tashi haikan wajen wayar da kan mutane sanin muhimmancin hakkinsu a kan shugabannin da hakkin shugabannin a kansu wanda hakan zai haifar mana da Nijeriya tagari”.

Ya karasa da cewa, “A PDM ba mu da masu kudi amma muna da masu zuciya, ba mu da ‘yan gani-na-iya amma muna da ‘yan siyasa, don haka ba mu shayin komai in dai za a yi shi a kan gaskiya. Mun fito don haskaka zukatan ‘yan Nijeriya da yardar Allah jam’iyyarmu za ta yi tsayin daka wajen tsayar da ‘yan takara nagartattu da jama’a za su yi na’am da su”.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI