Jam’iyyar APC Ta Yiwa PDP Tumɓur a Zaɓen Maye Gurbi A Legas — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Jam’iyyar APC Ta Yiwa PDP Tumɓur a Zaɓen Maye Gurbi A Legas

Published

on


A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne ɗan takarar jam’iyyar APC, Noheem Adams ya lashe zaɓen maye gurbi ta mazaɓar Eti-Osa da ke Jihar Legas, inda ya kayar da ‘yan takara takwas da suka fafata tare da shi.

Babban jami’I mai kula da zaɓen, Oyeyemi Oyedola ne ya bayyana sakamakon zaɓen a cibiyar tattara sakamako dake makarantar Firamare ta ‘Lagos State Model’, a ƙaramar hukumar  Eti-Osa.

Mista Oyedola ya bayyana cewa Adams na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u dubu 4,204 wanda suka bashi damar buge abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Arubiewe Abogun inda shi kuma ya samu ƙuri’u dubu 1,652.

Jami’in ya ci gaba da cewa; jam’iyyar AA (Action Alliance) ta samu ƙuri’u 10, jam’iyyar AD (alliance for Democracy) ta samu ƙuri’u 128, jam’iyyar BNPP ta samu ƙuri’u biyar, jam’iyyar DA ta samu ƙuri’a ɗaya, sai jam’iyyar PPA ta samu ƙuri’u takwas.

Mista Oyedola, wanda Farfesa ne, ya bayyana cewa adadin mutane dubu 183,551 aka yiwa rijista don jefa ƙuri’a. waɗanda aka tantance kuma mutum dubu 6,280, an samu ƙuri’u lafiyayyu guda dubu 6,015, an kuma yi watsi da ƙuri’u 154. Inda jimillan ƙuri’un da aka jefa suka kama dubu 6,169.

Farfesan ya ce; “Ni Farfesa Oyeyemi Elijah Oyedola, a matsayina na jami’in kula da zaɓen maye gurbi na mazaɓan Eti-Osa wanda aka gudanar a ranar 30 ga watan Satumban 2017. An gudanar da zaɓen kamar yadda doka ta tanada, inda ɗan takarar jam’iyyar APC Mista Adams Noheem Babatunde bayan ya cika duk wata ƙa’idar hukumar zaɓe, ya kuma samu ƙuri’u mafi rinjaye, dalilin haka nake ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen maye gurbin.” Kamar Farfesan ya bayyana da misalin ƙarfe 10:10 na dare.

Shi dai wannan zaɓen maye gurbin an gudanar ne sakamakon rasuwar da Kazeem Alimi, ɗan majalisan da ke wakiltar mazaɓar a majalisar dokokin Jihar Legas, yayi a ranar 18 ga watan Yulin 2017.

Advertisement
Click to comment

labarai