Connect with us

LABARAI

Kantoman Kudan Ya Cancanci Yabo -Surajo Bomo

Published

on


Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

‘Duk wanda ke lura da yadda aka sami kwanciyar hankali da kuma kawo ƙarshen yawan fashi da makami a ƙaramar hukumar Kudan da ke Jihar Kaduna, dole a yaba wa kantoman ƙaramar hukumar, Alhaji Shehu Mohammed na matakan warware waɗannan matsaloli a wannan yanki.

Wannan yabo ya fito ne daga matashin ɗan siyasan nan mai suna Alhaji Surajo Bomo, a zantawarsa da wakilinmu da ke Zariya, kan ci gaban da aka samu a batun tsaro a wannan ƙaramar hukuma ta Kudan.

Alhaji Surajo Bomo ya ci gaba da cewa, kafin Alhaji Shehu Mohammed ya kasance kantoman wannan ƙaramar hukuma, ba wai ɗan ƙaramar hukumar Kudan ba, hatta masu wuce ƙaramar hukumar da daddare suna wuce wa a cikin fargaban haɗuwa da ‘yan fashi da makami da sauran masu aikata muggan ayyuka da suke zuwa wannan yanki, suna tayar da hankalin al’umma.

Kan haka Alhaj Surajo ya buƙaci al’ummar ƙaramar hukumar Kudan da sauran al’umma da suke alaƙa da wannan yanki da su ci gaba da ba kantoman goyon baya, domin ya samu sauƙin aiwatar da kyawawan ayyukan da ya sa a gaba da suka shafi kawo ƙarshen ɓata-gari da suke cikin ƙaramar hukumar da kuma waɗanda ke zuwa ƙaramar hukumar domin tayar da hankalin al’umma.

Da kuma Alhaji Surajo ya juya ga iyayen yara da suke ƙaramar hukumar Kudan, ya tunatar da su cewar, akwai muhimmanci su kula da duk mu’amalolin da yaransu ke yi da sauran yara da suke wannan yanki, a cewarsa, idan har iyaye basu son a ladabtar da yaransu, ko idan an same su da laifi, basu son a yi masu hukumci, Alhaji Surajo Bomo ya ce duk wasu matakan tsaro da kantoma zai ɗauka, da wuya ya sami nasarorin da ya ke buƙata.

A ƙarshe, Alhaji Surajo Bomo ya kuma nuna gamsuwarsa da yadda jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda ke gudanar da ayyukan tsaro dare da rana a ƙaramar hukumar Kudan, ya ce, wannan ma ba ƙaramin al’amari ba ne da ya kawo ƙarshen ɓata gari a wannan ƙaramar hukuma ta Kudan.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI