Connect with us

MAZAN JIYA

Tarihi Da Gwagwarmayar Marigayi AVM Mukhtar

Published

on


Daga Abubakar Abba

Marigayi AVM Mukhtar Muhammed mai ritaya, shi ne Gwamnan farko lokacin mulkin Soja a tsohuwar Jihar Kaduna lokacin mulkin Soja na tsohon Shugaban ƙasa, Janar Olusegun Obasanjo mai ritaya.

Marigayin Mukhtar Muhammed, ya rasu  shekaran jiya Lahadi a wani Asibiti da ke ƙasar Landan bayan yayi fama da wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya.

An haifi AVM Mukhtar a ranar 11 ga watan Nuwambar shekarar 1944, ya kuma bar duniya yana

da shekara 73.

A halin yanzu, ‘yan uwa da abokan arziki suna ta zuwa gidan marigayin da ke cikin Birnin Kano domin yin ta’aziyya da jajantawa iyalansa dangane da wannan babban rashin da aka yi.

A bisa rahoton da wani ɗan uwansa mai suna Faruk Ɗalhatu ya wallafa a kafar sadarwa, ya bayyana cewa, marigayin ya rasu ne da yammacin shekaran jiya Lahadi.

Ɗalhatu ya bayyana cewa, Marigayi Mukhtar Muhammed, mutum ne mai haba-haba da jama’a mai son zumunci da taimaka wa dangi da kuma sauraron koken al’umma.

Marigayin, ya taɓa riƙe muƙamai da dama da suka haɗa da; Ministan Gidaje da Raya Birane daga shekarar 1976 zuwa shekarar 1977.

Marigayi Mukhtar Muhammed ya taka gagarumar rawa a juyin mulkin da aka yi wanda ya kawo tsohon Shugaban ƙasa na mulkin Soja, Janar  Murtala Mohammed kan karagar mulkin ƙasar nan.

Marigayin ya jagoranci kotun mulkin Soja da ta yanke wa ‘yan siyasa hukunci a lokacin Jamhuriyya ta biyu da aka zarga da cin hanci da rashawa a ƙarƙashin Mulkin Soja na Muhammadu Buhari daga shekarar 1983 zuwa shekarar 1985.

Bayan da aka yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari ta soja juyin mulki a shekarar 1985, Marigayi Mukhtar Muhammed an cire shi daga muƙamin da yake kai na gwamna; bayan da mulkin Tsohon Shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida Mai ritaya ta yi wa Muhammadu Buhari juyin mulkin.

An cire marigayi Mukhtar Muhammed daga muƙamin na Gwamnan Soji ne sakamakon saɓani da ya samu da waɗanda suka haɗa baki  aka yi wa Muhammadu Buhari juyin mulkin na cikin gida.

A shekarar shekarar 2002, Mukhtar Muhammed ya jagoranci gudanar da ayyukan ofishin yaƙin neman zaben Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na ƙungiyar (TBO).

A shekarar 2016, AVM Mukhtar Muhammed  ya zama Shugaban zartarwa na Jami’ar  Ahmadu Bello dake Zaria a Jihar Kaduna.

Tun kafin rasuwar sa, marigayin yana riƙe da sarautar gargajiya ta Wazirin Dutse dake cikin Jihar Jigawa.

Haka kuma Marigayin shi ne Mataimakin Shugaba na kwamitin amintattu na ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa(ACF).

Marigayi Mukhtar Muhammed shi ne kuma shugaban Rukunan gidan Rediyon Freedom da ke da shalkwata a Jihar Kano, daga bisani kuma ya kafa reshen gidan Rediyon a jihar Kaduna.

Bugu da ƙari, marigayi Mukhtar Muhammed ya taka muhimmiyar rawa wajen dawowa da Babban Birnin tarayyar daga Legas zuwa Abuja.

Marigayin ya riƙe muƙamin shugaba na farfaɗo da kayan noma na ƙasa a shekarar 1975. A shekarar 1975, marigayi AVM Mukhtar Mohammad, an naɗa shi a babban muƙami a Majalisar zartarwa ta Soji.

Har ila yau, Marigayin ya riƙe muƙaman shugaba a  Masaƙar Teryteɗ da kamfanin Dailfam da Kwalejin Zamani da ke Jihar Kaduna. Kuma ya riƙe Darakata na masana’antar kayan motoci dake jihar Kaduna.

Akwai abubuwa da dama da za a iya ci gaba da tuna marigayin Mukhtar Muhammed, musamman ganin ba  mutum ne nuna ban-bancin jinsi ba kuma yana son ganin ci gaban alummar ƙasar nan, musamman ‘yan Arewa.

Kuma mutum ne mai son ganin matasan ƙasar nan, musaman yankin Arewa, sun zamo masu dogaro da kawunansu.

A wata hira da aka yi  da marigayin ta ƙarshe a wani shirin gidan Rediyon Freedom dake jihar  Kano mai suna “Duniyar mu Ayau”, marigayin ya ja hanklin Musulmai wajen kasancewa cikin jin tsoron Allah ta hanyar neman ilimin addinin Musulumci.

Duk dai a cikin hirar, Marigayin ya koka akan talauci da jahilci da ya yi wa musamman wasu al’ummar Musulmi katutu, inda ya ce, hakan ya janyo ana barin su a baya.

A hirar marigayin, ya kuma yi tsokaci akan taɓarɓarewar ilimin zamani a ƙasar nan da rashin bin doka da oda da wasu ‘yan ƙasa keyi.

Bugu da ƙari marigayin a hirar ya yi kira ga gwamnatocin daka ƙasar nan dasu buɗe hanyoyin ayyuka, musamman don matasan ƙasar nan su samu sana’oin hannu da zasu zamo ma su dogaro da kansu.

Duk da cewar shi ne Shugaban Rukunin gidan Rediyonsa na Freedom, ba ya yi wa mahukuntan gidan Rediyon katsalandan wajen gudanar da ayyukansu.

Sakamakon kafa gidan Radiyon da ya yi, hakan ya bai wa ‘yan Arewa da suka karanta aikin Jarida dama waɗanda ba ‘yan Arewar ba damar ɗaukar su aiki don su nuna tasu bajintar.

Marigayin ya rasu ya bar mata ɗaya da ‘yaya da dama da kuma jikoki. Har ya zuwa haɗa wannan rahoton, ana dakon jiran gawar marigayin don yi masa zana’ida a bisa tsarin Musulunci. Allah ya yi masa rahama amin.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI