Connect with us

KASASHEN WAJE

Ƙasashen Waje Wanda Ya Kai Harin Las Ɓegas Me Ya Hana A Kira Shi Ɗan Ta’adda?

Published

on


Ɗaukar makami a shiga cikin al’umma a kasha su ko a jikkata sub a abu ne faru ba, iila dai kawai ana kallon masu yin kisan kai ta fuska biyu.  Fuska ta farko idan wanda ya yi kisan sunansa yana da alaƙa da na Musulunci ko musulmi sai a kira shi da Ɗan Ta’adda, ko da bai yi nasarar kisan ba, kuma ko da kuwa shi ba Musulmin ba ne, daga nan an fara yamaɗiɗi da shi a kafofin yaɗa labarai kenan.

Ɗaya fuskar kuma, idan aka samu wani ya farmaki wasu mutane ya kashe ko jikkata, matuƙar sunansa ya saɓa da na Musulmi, kuma ya tabbata ba musulmin ba ne, sai ka ji ana cewa ai ɗan bindiga daɗi ne, ko kuma ace shi mahari ne.

Shekaru kusan uku da suka gabatawani ɗan asalin ƙasar Faransa ya kai hari kan wasu mutane, ya yi nasarar kashe kusan mutum ɗari, amma da aka kama shi, sai aka riƙa nuna shi a matsayin ɗan bindiga daɗi. Shi da kansa yake faɗa a yayin da ‘yan jarida suke hira da shi cewar “ Da ni Musulmi ne da sai a kira ni da ɗan Ta’adda.”

Wannan shi ne abin da ya faru a ƙasar Amurka a jihar Jihar Las Ɓegas kwanan nan, lamarin da ya shayar da duniya mamaki. Wanda har ta kai ga Ƙungiyar IS ta fito ta fara bayyana maharin da cewa ɗanta ne, har ma wai ya Musulunta kafin ya kai harin, don dai wannan suna ya ci gaba bin Musulmi.

A yanzu a Amurka muhawara ta ɓarke a kafafen sada zumunta game da abin da ya hana a kira Stephen Paddock da sunan dan ta’adda.An bayyana maharin, mai shekara 64 ne da sunaye kamar: “tsohon akanta” “kaka” “ɗan caca” “mahari” da “wanda ya kitsa kai harin shi ɗaya”, amma babu wanda ya kira shi da sunan ɗan ta’adda.

Har yanzu ba a san dalilin da ya sa shi kai harin ba. Sai dai ba shi da wata dangantaka da wata ƙungiyar ‘yan ta’adda kuma babu wani abu da ya nuna cewa yana fama da matsalar taɓin hankali.

A kafafen sada zumunta, mutane da dama sun ce idan da a ce Mista Paddock Musulmi ne, to da za a rika kiransa da sunan “ɗan ta’adda”  Cikin hanzari ba tare da samun waɗansu hujjoji da suka alaƙanta shi da masu tsananin kishin Islama ba.

Fitattun mutane da suka haɗa da malaman jami’a da ‘yan wasan kwaikwayo da mawaƙa suna ci gaba da tambaya game da abin da ya hana a danganta maharin da ta’addanci.

Kamar yadda dokar jihar Neɓada (wato jihar da aka kai harin) ta bayyana ta’addanci: ta ce “ ta’addanci shi ne duk wani aiki da ya tada zaune tsaye, wanda ya jawo babbar cutarwa ga jiki, ko asarar rai ga al’umma.”

Haka jama’a suka rika wallafa sashen dokar jihar da yake magana kan ta’addancin. Duk da waɗannan abubuwan da suka bayyana ƙarara, Shugaban ‘Yan sanda na birnin Las Ɓegas Joseph Lombardo yayin taron manema labarai game da maharin ya ce: “ Ba mu da amannar game da aniyarsa. A yanzu, mun yi amanna cewar shi kaɗai ya kai harin.”


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI