Connect with us

MANYAN LABARAI

Asibitin Fadar Gwamnati Zai Koma Na Kuɗi

Published

on


Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa, Mista Jalal Arabi, a jiya Laraba ya bayyana  cewa hukumar asibtin Fadar Shugaban Ƙasa, za ta nemi damar mayar da asibtin na kuɗi, domin a magance wasu matsaloli da ke addabrsa.

Wannan jawabin ya fito ne daga wata sanarwar da mataimakin daraktan yaɗa labarai, na fadar shugaban ƙasa, Mista Attah Esa ya fitar, inda sakataren ya mayar da martani ga wasu rahotanni da ke fitowa kwanakin baya daga kafafen watsa labarai.

Arabi ya bayyana cewa mayar da asibitin zuwa na kuɗi zai bayar da wata dama na samar wad a asibitin da hanyar samun kuɗaɗen shiga da kuma rage wa gwamnatin tarayya nauyin kuɗaɗen da take ware mishi, ba kamar yadda a baya a ke tafiya ba, inda ake yi wa kowa aiki kyauta.

Ya yi alƙawarin cewa za a sauya wa asibitin fasali, ta yadda komi zai zama ingantacce kuma mai nagarta.

Ya ce: “Wannan asibitin, shi ne kaɗai a babban birnin tarayya, asibitin da majinyata ke ziyarta a duba su ba tare da an caje su ko ƙwandala ba.

“A wasu asibitocin gwamnati da ke Abuja, akan buƙaci mutane da su biya kuɗin duba su da ƙwararru zasu yi, yi musu magani, gwaji, da sauransu, amma a lamarin ba haka yake ba a asibitin fadar shugaban ƙasa.

“Asibitin na fadar shugaban ƙasa ba ya cazar ko ficika, babu wanda ke biyan hatta kuɗin buɗe kati, balle na sauran lamurran da suka shafi duba mara lafiya da rubuta magunguna. Wanda wannan wani nauyi ne da kullum yake ƙara ƙaruwa a kan asibitin.

“Mu na da kayan aiki masu inganci da nagarta a ƙasar nan. Alal misali, a duk wata muna kashe kusan miliyan biyu domin kula da injunan gwaji da injin MRI. Duk da haka babu wani gwaji da muke cazar mutane idan sun zo a yi musu.

Arabi ya ƙara da cewa, sai dai, a wannan sabon tsarin da suke son kawo wa, za a tantance waɗanda za a duba, ta yadda marasa lafiya da ke da rajista da hukumar NHIS ne za su samu wannan tagomashin.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI