Connect with us

KIWON LAFIYA

Matsalar Rashin Yin Karin Kumallo

Published

on


Daga Mustapha Hamid

Binciken masana fannin lafiya ya fayyace cewa, mutanen da suke ƙin yin karin kumallo, ko kuma suke sakaci wurin yin sa yadda ya kamata, kama daga yin karin kumallon da abinda yakamata, ko kuma lokacin yin, sun fi daman kamuwa da cutar daskarewar manyan hanyoyin Jini da suke dakon Jini daga Zuciyar Mutum, zuwa sauran sassan jikinsa, wanda hakan kuma kai tsaye yana haifar da babbar illa da kuma sabbaba ciwon Zuciya.

Binciken da Jaridar kiwon lafiya ɓangaren matsalolin da suka shafi Zuciya da ke Ƙasar Amurka su ka yi, sun gano cewa, sai manyan Jijiyoyin dakon Jinin Bil’adama sun gama daskarewa da lalacewa da daɗewa, sannan alamomin ciwon Zuciya ke bayyana.

Masu binciken sun bayyana cewa, abubuwan da suka gano yayin binciken zai taimaka matuƙa wajen yaƙi da ake yi da cututtukan da suka danganci Zuciya, wanda ya fi kowane irin cuta laƙume rayukan Bil’adama, wanda yayi sanadin mutuwar aƙalla Mutane  miliyan 17.7 a shekara ta 2015.

Mutanen da suke ƙin yin karin kumallo, sun fi waɗanda a kullum suke yin karin kumallon samun matsalolin rashin lafiya, kamar yadda marubuci, kuma mai yin bincike a fannin matsalolin Zuciya Mr. Ɓalentin Fusta ya wallafa.

Wannan bincike, yana ƙunshe da shaidun da suke tabbatar da cewa, mummunar al’adar nan da wasu Mutane suke yi, na ƙin yin karin kumallo, idan har suka canza daga hakan, to za su iya kaucewa ɗimbin matsalolin cututtukan da ka iya kama da kuma sabbaba musu ciwon Zuciya.

Binciken, an gudanar da shi ne a kan Mutane 4000, masu matsakaicin shekaru, kuma dukkanin su ma’aikata a Ƙasar Spaniya.

Binciken, ya bibiye su har na tsawon shekaru 6, inda kowanne 1 cikin Mutum 4 suna cin Abinci mai sanya ƙarfi ne yayin karin kumallo, wanda yake ƙunshe da kaso 20% ko fiye, na abububwan da ke sanya ƙarfi ga jikin Bil’adama a gaba daya yini.

Mafi yawancin Mutanen da aka gudanar da binciken a kan su, kimanin kaso 70 cikin 100 suna cin abubuwan da suke ɗauke da abubuwa masu rangwamen saka ƙarfi ga jikin Bil’adama da bai haura kaso 5% ba.

Kaso 3 kuma cikin su sun ce, ba sa yin karin kumallo, ko kuma su na yi kaɗan kaɗan, wannan kaso binciken ya gano sun fi ragowar fama da matsalolin rashin lafiya, da kuma kamuwa da nau’ukan ciwuwwukan da suke da alaƙa da Jijiyoyin Jini da na Zuciya.

Waɗanda ba sa yin karin kumallo kwata-kwata an gano suna fama da matsalolin da suka shafi yanayin  girma, da kuma ƙirar Ƙugunsu, yanayin nauyi da ƙiban su, da hauhawan jini, da kuma abubuwan da suke sabbaba ciwon Sukari.

Akwai bincike masu yawa da aka gabatar a baya da suka nuna cewa, yin ingantaccen karin kumallo yana da alaƙa kai tsaye da ingancin ƙoshin lafiya, kamar yadda wasu binciken suka nuna cewa, rashin yin karin kumallon suna sabbaba manyan matsaloli da cututtukan hanyoyin jinin bil’adama.

Farfesa a fannin kimiyyar magunguna na Jami’ar Kalifoniya da ke Ƙasar Amurka, Mr. Prakash Deedwania, ya tabbatar da cewa, duk da cewa mutanen da ba sa yin karin kumallo ba su fiye fama da matsalar cutar ƙiba ba, amma dai rashin yin karin kumallon yana da matuƙar illa ga kiwon lafiyar bil’adama.

“Karin kumallo, shine Abinci mafi muhimmanci da Ɗan adam ke ci a tsawon rana”


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI