Connect with us

RA'AYINMU

Ɓarayin Amfanin Gona Sun Addabi Manoma

Published

on


Daga lokacin da gwamnatin canji a ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari ta hau mulki zuwa yau, kowa ya san irin yadda ta riƙa nanata batun muhimmancin noma ga cigaban ƙasar nan.

Tunda gwamnati ta lura cewa babbar hanyar da Nijeriya take samun kuɗaɗenta masu tsoka ta kasuwar mai a duniya ta toshe, sai ta fara neman hanyoyin da za ta bi ta ɗauke dogaron tattalin arziƙin ƙasar a kan mai zuwa wasu sassa da suka haɗa da aikin gona, da ma’adanai, da haɓaka karɓar kuɗin haraji da sauran su.

Gwamnatin ta ƙaddamar da shirye-shirye daban-daban a kan yadda za ta haɓaka aikin gona ba domin wadata ƙasar nan da abinci ba har ma da fitarwa zuwa waje. Wannan ya sa ta yi wani shiri na musamman na haɓaka noman shinkafa a Kebbi ta hanyar baiwa manoma da ‘yan kasuwan da za su yi hada-hadar shinkafa bashin zunzurutun kuɗi Naira bilyan 200 ta hannun Babban Bankin Nijeriya (CBN). Bugu da ƙari ta ɓullo da wata sabuwar dabara ta shigo da ‘yan kasuwa cikin harkar noma wadda a ƙarƙashinsa ‘yan kasuwan ke baiwa manoma rance su yi noma idan lokacin girbi ya yi kuma su bi su har gonar su saye amfanin gonan domin rigakafin cewa manoma sun yi noma an bar su da kayansu babu masu saye. Sunan shirin ‘Anchor Borrowers’ a turance.

Manoma na birni da karkara sun samu damar nunfasawaa saboda yadda gwamnatin ta nuna cewa da gaske take a kan shirinta na haɓaka noma. Sai dai kuma, ga dukkan alamu murnar manoman na neman komawa ciki saboda irin fitinar sace-sace da ɓarayin amfanin gona suka tasa su a gaba da ita.

Tun daga lokacin da amfanin gona musamman masara da doya suka fara nuna, kimanin wata ɗaya zuwa biyu da suka gabata, manoma sun kasa yin barci da idanunsu biyu a rufe.

Musamman a yankunan karkara da abin ya fi ƙamari, manoma sukan gama shan wahalarsu a gona suna aiki tare da kula da abin da suka shuka suna jiran lokacin girbi ya yi, a tsakanin ɗan wani lokaci kaɗan sai ɓarayin amfanin gona su bi dare su yashe musu gona kaf!

Lissafa manoman da irin wannan rashin imani na ɓarayin ya sa suka zubar da hawaye suna nan bila’adadin a kusan kowace jiha musamman a yankin Arewa.

Bisa wani binciken da wakilanmu suka gabatar, akwai wasu manoma masu matsakaicin ƙarfi a yankin Kudancin Kaduna da suka riƙa ɗaukan masu gadi aiki suna masu gadin amfanin gonar da suka shuka. Wannan bala’i da me ya yi kama? Su kuma ƙananan manoman da suke neman na sakawa a bakin salati da suka noma gonarsu ‘yar kaɗan an bar su ko oho, domin abin da za su ci suke nema ballantana kuɗin da za su biya wani ya yi musu gadi a gona.

Irin wannan ɓarna da ɓarayin amfanin gonan ke yi tana haifar da illoli na sarari da na ɓoye. Ta haddasa cire amfani gona barkatai tun bai ƙosa ko gama nuna ba. Ta sa wasu ƙananan manoma hawan jini saboda ɗan abin da suke tunanin tanada wa iyalansu wajen ciyarwa an raba su da shi kuma ba su da ƙarfin yin noman rani, kana a halin yanzu damina tana dab da yin sallama sai ta baɗi. Tana dakushe ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da wadata ƙasa da abinci, domin hatta waɗanda suke noma ba don sayarwa ba ɓarayin sun cire musu sha’awar noma. Ƙara haifar da tsadar farashin amfanin gona a cikin ƙasa saboda ƙaruwar zuwa nema a kasuwa tunda wanda suka noma (manoman na ainihi) an kassara su. Sannan hakan alama ce ta ƙaruwar aikata laifuka a ƙasa. Illolin sace-sacen amfanin gona tun kafin girbi ga manoma suna nan birjik ba za su ƙidayu ba.

A lokutan baya, an san cewa idan manomi ya yi girbi sai ya bar amfanin gonarsa a gona ba tare da ya kwashe zuwa rumbunsa na gida ba har ya kai tsawon wani lokaci, ɓarayi za su bi baya su yashe abin da ya girbe kaf. Sai a ce masa shi ya ja tunda ya girbe ya bar shi a gona haka kurum. Amma a wannan zamanin sai gashi tun kafin a girbe amfanin gonan ake bi har cikin gonar ana sacewa.

Lallai ya kamata gwamnatin canji ta kawo wani canji da zai dama wa ɓarayin lissafi a wannan harkar da suke yi ta karya manoma da noma.

Gwamnati ta ɓullo da wani haɗin kai a tsakanin sarakuna da dakatai da masu kula da kasuwanni ta yadda za a riƙa gano cewa idan mutum ya kawo amfanin gona kasuwa, za a fahimci satowa ya yi koko nasa ne? Gwamnati ta ƙarfafa malaman gonanta su riƙa baiwa manoma shawarwari a kan yadda za su riƙa amfana da abin da suka noma tun kafin ɓarayi su fara musu ɓarna. Sannan su ma jama’ar gari su ba da haɗin kai, kar su sayi kayan sata kuma duk wanda aka gani a kai rahotonsa ga hukuma domin hukunta shi.

Haƙiƙa idan aka yi wannan manoma za su numfasa, noman da ake so ya zama ɗaya daga cikin ginshiƙan tattalin arziƙin ƙasar nan ya bunƙasa tun daga yankunan karkara har zuwa masu manyan gonakai. Masu karin magana dai sun ce “asara ko ta miyawun baki ce ba ta da daɗi!”

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI