Connect with us

DAN JARIDA

Mai Ɗaukan Hoto Na Jarida Hannu Biyu Yake Aiki — Abdullahi

Published

on


Ɗaukar hoto yana da muhimmiyar rawa da yake takawa a ɓangaren aikin jarida. Duk wata jarida da ta amsa sunanta ba ta cika sai da hotona masu ƙara fito da labaran da take bayarwa. Hasalima, masana sun bayyana cewa hoto a aikin jarida na iya bayyana labari fiye da kalomomi dubu da za a rubuta.

Saboda muhimmancin hoto a aikin ya sa a wannan makon muka ɗora wani shahararren maɗaukin hoto a ɓangaren aikin jarida a kan kujerar Ɗan Jarida A Bakin Aiki. Wannan kuwa shi ne Isah Abdullahi, haifaffen garin Minna a Jihar Neja wanda ya yi karatunsa na faramare har sakandare duk a nan Minna. Ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi ɗaukar hoto a ɓangaren aikin jarida da kuma yadda yake aika wa kafafen yaɗa labarai daban-daban da hotuna.

Ya kwashe tsawon shekaru goma yana sana’ar ɗaukar hoto a babban filin taro na ƙasa (Eagle Sƙure) da ke Abuja, daga bisani ya samu aiki da kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Jihar Neja a matsayin mai ɗauko hotuna wanda ake amfani da su a mafi yawan kafafen yaɗa labarai na gwamnati, wanda har ila yau bai tsaya nan ba yakan kuma aike wa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.

Saboda iya ɗaukan hotonsa, hatta hukumomin tsaro na muradin aiki da shi musamman rundunar tsaro ta ‘yan sanda da soja da ke Minna, fadar gwamnatin jihar. Ƙwazonsa ya sa rundunar ‘yan sanda ta taɓa ba shi lambar yabo a matsayin ɗan jarida mai ɗaukar hoto mafi ƙwarewa.

Isah Abdullahi ya bayyana wani aiki da ya taɓa yi mai hatsari amma kuma abin ya yi nasara.

“Mun shiga daji tare da sojoji lokacin da barazanar ɓarayin shanu ya fara zama barazana ga mutanen karkara, lokacin da na hango mutane ban gane su ba su ma sojojin ma ba su gansu ba, na karkata da kamara ta na ɗauki hoto na cikin hikima kuma hoton ya ratsa duniyar kafafen yaɗa labarai sosai”.

Abdullahi ya kuma bayyana yadda ya yaɓa fuskantar barazana da tozarta har ya kusa rasa kamararsa ta aiki amma kuma hakan sai ya zamo mashi alheri.

“A lokacin gwamnatin da ta shuɗe ta Dakta Babangida Aliyu ta kafa kotun musamman kan binciken gwamnatin marigayi Injiniya Abdullahi Abdulƙadir Kure, na ɗauki wani hoto lokacin da aka zo da marigayin gaban kotun binciken, sai wasu makusantan shi suka ga cewar lallai idan na sake aka buga hoton nan a jarida kamar akwai tozarci gare shi, bayan an tashi daga kotun na fara fuskantar barazana amma sai shi marigayin ya ba su shawarar cewar ba a yiwa ɗan jarida abin da suke son yi fa, mai makon hakan, na dawo gida da dare suka rutsa ni ta hannun wani ɗan uwana haka, aka nemi alfarmar in goge hoton nan dan kar ya fita, sai na ga cewar gwamnati fa nake wa aiki kuma jami’an gwamnatin ne suka umurce ni da hakan, kawai nan ta ke na goge hoton”.

Abdullahi ya banbanta masu rubuta labari da masu ɗaukar aiki.

“Kwatanta ɗan jarida mai ɗaukar hoto da mai rubuta labari gaskiya akwai bambanci sosai ma, domin kai mai rubuta labari za ka iya zama a waje kila kana da na’aurar naɗar bayanai sai kai aikin ka ba a sani ba, amma mai ɗaukar hoto kuwa duk inda ka ratsa an sani saboda yanayin kayan aikin mu masu muhimmancin na da tsada sosai dole muke amfani da waɗannan masu girman.

“Bayan haka mu ma tudu biyu muke ci, bayan ɗaukar hoton ma mukan baiwa wasu ‘yan jaridu cikakkun labarai ganin kowanw lokaci mukan kasance a gaba-gaba dan samun cikakken labarin abin da ya kamata mu ɗauka hoton, sau da yawa akan zaunar da mu dan ba da labarin hoton da muka kawo daga nan sai ka ga an gina labari kuma ya tafi yadda ya kamata”.

Ƙwazo da jajircewa kan sanya mutum zama gwarzo a aiki. A cewarsa Isah, “Ni ma kuma na ga alfanun hakan domin lokacin da PDP ke kan mulki a koda yaushe ina halartar shirye-shiryensu kuma ina samo hutuna sosai, sai wata rana aka kira ni, aka ce min lallai PDP ta yaba da ƙwazon da na ke nunawa a aiki, dan haka ta karrama ni da sabon mashin na hawa Suzuki, bayan nan na samu kyaututtuka da lambobin yabo masu yawa.

“Mafi yawan lokaci akwai abin da ke samun mutum a yanayin aikinsa na jin daɗi ko akasin sa. Hm! Haka ne kam, mun fuskanci ƙalubale amma mai makon yasa mun samu karayar zuciya, sai abin ya zama kamar amma mana allura ne na ƙarin ƙwazo, wanda hakan yasa na auri matata, na sai motar hawa, na sai filin da ni ke muradin ginawa, ka ga ai ba zan manta da hakan ba kuwa, yau ina da shekaru goma sha ɗaya a ƙarƙashin gwamnati a matsayin ma’aikaci mai ɗaukar hoto, a ɗan shekarun da na yi na aiki na yi aure, na sai mota, na sai fili ka ga ke nan akwai yiwuwar zan iya gina gida kafin lokacin barin aikin kenan, saboda haka ni ƙalubalen da na fuskanta taki ne gare ni shi yasa ban cika tuna wahalhalun da na sha a aikin jarida ba sai dai daɗin”.

A lokutta da dama, yanayin aiki kan jefa mutum a wani yanayi na rashin lafiya ko faɗawa wani halin ƙunci na rayuwa, amma ya abin yake ga Malam Isah.

“Lallai ni kam ga da daman abokan aikina suna kokawa akan matsalar Ido, kasan ita kamara tana da na’urar hangen nesa wanda da shi mai aikin ɗaukar hoto ke anfani da shi wajen zuƙo abinda yake son ɗauka hoton, wannan na’urar ita mu ke cewa Makuri, tau idan wasu zasu ɗauki hoto musamman da rana suka sanya idon su inda za su hango mutum, wannan na’urar makuri ta yi dace da gefen rana, zuƙo ranan nan yakan shafi idon mutum, yakan yiwa mutum lahani sai ya fara gani buji-buji haka daga in yayi rashin dace wannan idon ya samu matsala ke nan, ni kan ina kiyaye wannan saboda daɗewa ta a harkar”.

Yabo ko karramawa yakan biyo bayan ƙwazo da natijir da mutum yake nunawa a wajen aiki, shin Malam Isah a na shi ɓangaren me ya janyo mai wannan?

Ya ce, “Ai shi aikin ɗaukar hoton jarida ya bambamta da ɗaukar hoton suna ko bukin aure. Domin a suna ko aure ana ɗaukar kwambar jama’a ne kawai, amma hoton jarida akan so ɗaukar yanayi ne da in ka kalla shi ɗin ma hoton zai baka labarin wani abu da ka ke kokwanto ka gane, misali hoton da na faɗa ma na ɓarayin shanu da na faɗa ma idan ka ga kafafen yaɗa labarai da sukai anfani da shi suna da yawa, amma babban abin baƙin ciki idan aka yi anfani da kayan ka ba a baka ladar aikin ka, misali idan ba jaridun gwamnatin jiha ba, ba ɗan jaridar da za ka baiwa hoto yayi anfani da shi ya rubuta cewar kai ne ka ɗauko hoton wanda wannan yana da ciwo matuƙa”.

Idan ka yi la’akari da yadda ‘yan yanar gizo sukai yawa kuma ana ɗaukar hotuna da wayoyi, shin hakan bai ma aikinku illa ba kuwa?

“Ai kowani da bigirensa ka gane, duk wanda yasan jarida yasan martabar jarida har gobe ya san ba makwafin jarida, illa yanzu wata hanya ce ta ɓullo a zamanance ga ‘yan jarida raggaye da su tashi tsaye su ƙara ɗamara sosai, domin akwai labarai har yanzu masu tasiri a wajen jama’a, amma mai tunanin yaci bilis a aiki sai ya gyara ɗamara wannan lokacin ya wuce, shi yasa sau da yawa idan ka ɗauki jarida kana karantawa sai ka ga ba labarin bayarwa abin ya koma kame-kame, idan ka ɗauki jaridar Newsline ta asabar ɗin makon jiya itace kaɗai ta kawo labarin kashe jami’an sojoji da ɓarayin shanu suka yi a dajin Alawa, amma akwai ‘yan jarida sama da arba’in da ke wakiltar kafafen yaɗa labarai daban-daban suna zauke suna jiran sai an kira su an ba su kuɗi, to ka ga wannan harkar yanar gizo su yayi masu illa ke nan tunda daman raggaye ne.”

Ganin a ɓangare ɗaukar hoto kusan ba ‘yan jarida da yawa, amma me ya kawo hakan.

“Dole ne ai, domin shi aiki ne da ke son ƙwazo da gogewa da rashin tsoro, mafi yawa sun fi son aikin da za a zama ‘yan ƙwalisa idan an tafi aiki a samu wuri a zauna, amma mai ɗaukar hoton jarida bai da wajen hutawa, a ko yaushe jikin da ƙwaƙwalwar shi suna aiki ne, yana tunanin abinda zai samu da yafi na baya, dan haka za ka ga yana ta yawan zagaye-zagaye dan tabbatar da abinda yake buƙata.

Zai yiwu a kwatanta hoto da ita jaridar kacokan?

“Ta ina ai shi hoto zuciyar jarida ce, ka dubu mujallu ko jaridu har kan talabijin za ka ga hotunan su ke ƙawata labaran kuma sune ke janyowa ita kanta jaridar kasuwa. Saboda haka gudunmawar da hoto ke bayarwa a aikin jarida yafi ƙarfin kwatantawa, misali dubi ‘yan gidan talabijin har da kwalliya ake masu dan hotunan su yi kyau sosai ko, sannan ka dubu hotunan da ake bugawa a jarida idan ba su magana sai ka tarar akwai saƙon da suka aikawa jama’a, dan haka hutuna suna da rawar takawa sosai a aikin jarida.

“Shi yasa a kullum na ke cewa masu tasowa bayan ka tafi makaranta ka karanta aikin jarida, nemi ƙwararru a aiki ka jingina da su sai ka anfani abinda ka ke muradi a rayuwa, shi karantun yana da anfani ga mai aikin gwamnati, amma ƙasashen da suka cigaba ba su damu da kwalin ka ba illa ƙwarewa, ba kuma za ka ƙware ba sai ka jinginu da ƙwararru ka zama almajirinsu.

Kowani ɗan Adam na da buri a rayuwarsa, shin Malam Isah me ye burinsa a wannan aikin?

“Gaskiya ba ni da burin da ya wuce in samu fice sosai a wannan aikin na wa, ina son zama cikakken mai ɗaukar hoto ga kafafen yaɗa labarai da za a yi gogayya da shi a ko ina a duniya. In samu kayan aiki irin na zamani da zai ba ni damar nuna bajinta ta a harkar hoto”.

tare da Muhammad Awwal Umar

email:[email protected] 08093947702

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI