Connect with us

ADON GARI

RAINO DA TARBIYYA: Illar Fita Aikin Iyaye Ga Tarbiyya

Published

on


Fita zuwa wajen ƙwodago da iyaye maza da mata ke yi yana babbar illa ga raino da tarbiyyar ‘ya’yan mu a wannan zamani ta hanyoyi da dama:

Yara suna tashi babu cikakkiyar kula na tarbiya daga iyayensu musamman iyaye mata. Da zarar uwa ta haihu tana nan tana fargaban hutun da aka bata a wajen aiki taƙaitacce ne, don haka idan ya ƙare yaya za ta yi da abin da ta haifa? Daga nan sai tunani a kan ina za ta samu wacce za ta kula da jariri ko jaririya kuma wani irin abinci za ta tanada don bari a gida? Da dai sauran abubuwan da za su biyo baya bayan komawa ofis.

Rashin ba da cikakken lokaci (kula) ga ‘ya’yan mu yakan janyo rashin shaƙuwa da juna. Wanda haka ya zamo wani babban giɓi a rayuwar mu, dalilin rashin zama tare da yara ya sa har wasu yaran sukan ƙi shan nono (maman uwa) sai abincin gwangwani wanda shi ma rashin shan nono na rage shaƙuwa da sabo da iyaye, kasancewar ta hanyar shan nono akan samu wata alaƙa ta ƙara danƙon soyayya a tsakanin mahaifiya da jariri ko jaririyarta. A dalilin haka za ka ga wasu yaran har sun fi son su yi kusa da ‘yar aiki fiye da uwar da ta haife su domin sun fi zama na tsawon lokaci tare.

A zamanin da, lokacin da muka taso ya kasance ba ma iya zuwa ko ina kamar misalin yawan bin gidajen ƙawaye, saboda sabo da zama a cikin gida tare da iyayen mu, idan har za a je ziyara dole sai da izinin iyaye kuma sai an tabbatar da irin yarinya ko yaro da ake ƙawance da su kuma an san gidan da suka fito kafin a yarda. Hakan ya saɓa da wannan zamani da muke ciki, inda yara sai dai su tashi kawai (musamman idan iyaye suna ofis) su kama hanya da sunan za su ziyara, daga nan sai dai a ji su a wani gari ko wata unguwa dabam. A irin hakan an sha samun labarai marasa daɗi ta yadda wasu lokutan ma sai dai a ji yara sun je gidajen abokanansu sun yi ma iyaye ɓarna ta hanyar yin sata ko ɗaukar moto su fita ba tare da izini ba.

Ina kira ga iyaye mata da mu fito da wani tsari na musamman don ganin mun ba wa ‘ya’yan mu kula da tarbiyar da ta dace ta wasu hanyoyi kamar haka.

(a)    Ganin gwamnati ta sake tsarin ba da hutun haihuwa ta yadda aƙalla uwa za ta iya zama a gida ta kula da abin da ta haifa na tsawon watanni shida (6) kafin komawa ofis, Uwa ta yi ƙoƙarin tabbatar wannan zaman hutun da za ta yi a gida ba abin da za ta ba jariri sai ruwan nono (mama) kawai.

(b)    Uwa ta tabbatar ta karanci wacce za ta bari da raino sosai da sosai ta wajen tsafta, da addini da kulawa da dukkan hidimar da ta  shafi yara kafin ta koma aiki.

Ya ku ‘yan’uwana iyaye mata, wajibi ne mu san cewa ‘ya’yan mu jarin mu ne kuma rabin ran mu ne! Don haka mu basu kulawa ingantacciya. Allah ya bamu sa’a. Mu haɗa a mako mai zuwa, insha Allah

 

Amira Rakiya Bamalli

08094233473

[email protected]


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI