Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Gwamnonin Farar Hula A Kano: Wa Ya Biya Bashi, Wa Ake Bi?

Published

on


Daga Maje El-Hajeej Hotoro, Kano

Tarihin Siyasar Kujerar Gwamnan jihar Kano

Marigayi Alhaji Abubakar Rimi (1979-1982) shi ne ɗan zaɓaɓɓen gwamnan farar hula na farko a tarihin siyasar tsohuwar jihar Kano. Kana kuma gwamnan siyasa na farko da ya kafa tarihin muhimman ayyukan raya ƙasa da a yau jihar ke alfahari da su. Sannan kuma gwamnan siyasa na farko da ya assasa siyasar gwagwarmayar ƙwatowa talaka ‘yanci. Gagarabadan da ba ya shakkar taka duk wani shafaffe da mai matuƙar ya karya doka. Gagaren da ya shafawa talakawa toka a ido ga daina shakkar duk wani ɗan kama-karya.

An buga tamburan siyasa an kuma lale katin adawa. Tafiya sannu kwana nesa, wutar rikicin cikin gida na jam’iyya ya kunno kai, wanda Hakan ya sa dole Rimi ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PRP da ya ci zaɓe zuwa NPP. Rimi ya sauka daga muƙaminsa sakamakon sauya jam’iyya da ya yi. Wanda Hakan ya ba wa mataimakinsa Audu Dawakin Tofa ci gaba da riƙe kujerar domin fuskantar zaɓe na gaba. Duk da ruwan fitattun ayyuka da Rimi ya malalawa Kanawa Hakan bai sa sun ƙara zazzaga masa ruwan ƙuri’u ba a yayin da ya ƙara neman kujerar a 1983 ƙarƙashin jam’iyyar NPP.

Sabo Bakin Zuwo da jam’iyyar PRP ta tsayar shi ne ya lashe wannan zaɓe duk kuwa da jam’iyyar NPN mai mulkin ƙasa ta turo Aminu Wali ya nemi wannan kujera. Kanawa sun zaɓi Sabo Bakin Zuwo ne saboda biyayya ga jam’iyyar PRP da kuma jagoranta Malam Aminu Kano ba wai domin ya fi Rimi cancanta ba. Kazalika maƙudan kuɗaɗe da Aminu Wali ya narkar a wancan lokacin ko kaɗan bai yi tasiri wajen hana Kanawa bin ra’ayin su ba.

An zargi Sabo Bakin Zuwo da assasa siyasar ramuwar gayya da kuma salon mulkin rashin manufa. Ana tsaka da warwasa siyasa ne Janar Muhammadu Buhari ya taka musu birki ta hanyar yin juyin mulki a shekarar 1983.

Bayan Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya hamɓarar da gwamnatin Buhari ya assasa salon siyasar da duk duniya haramtacciya ce wacce ake yi wa laƙabi da Ungulu da kan Zabo. Gwamnoni da ‘yan majalisar jiha duk zaɓaɓɓun ‘yan siyasa ne yayin da kuma ministoci da shugaban ƙasa kuma duk sojoji. Lokaci guda Babangida ya haɗa kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokokin soja.

A wannan yanayi ne Kabiru Ibrahim Gaya ya zama gwamnan jihar Kano na tsawon shekara biyu daga 1990 zuwa 1992 ƙarƙashin jam’iyyar NRC.  A wannan lokacin Kabiru Gaya ya buga takarar ne da Injiniya Magaji Abdullahi a ƙarƙashin jam’iyyar SDP wanda attajiri ne da kuɗinsa suka gaza mallaka masa wannan kujera.

Kabiru Gaya ya yi salon mulkin da Kanawa ke yi wa laƙabi da Insha Allahu. Domin a lokacin duk wani alƙawari da ya ɗauka zai faɗi Insha Allahu amma kuma aka riƙa kallon hakan da ta tsaya ne kawai a iya fatar bakin sa.

Gwamnatin soji ta marigayi Janar Sani Abacha ya yi tafiyar ruwa da wa’adin mulkinsu sakamakon juyin mulki da ya yi. A lokacin da wasu gungun ‘yan siyasa suka haɗa ƙarfi da ƙarfe su ka kori mulkin soja a ƙasar nan jam’iyyar PDP ta zama jam’iyya mafi ƙarfi da tasiri a duk faɗin Nijeriya, a jihar Kano an ga tasirin PDP domin iyayen da su ka yi naƙudar ta irinsu Dakta Abubakar Rimi da Malam Musa Gwadabe da kuma Alhaji Aminu Wali su ka yi taimakekeniya gurin kafa mulkin PDP a Kano wanda Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama Gwamna a shekarar 1999 ya kuma ƙare a shekarar 2003.

A tsawon mulkin PDP a Kano an samu saɓani da rabuwar kai a tsakanin iyayen jam’iyyar da kuma mabiya, wannan yaƙi na cikin gida ya taimaka wajen watsewar jam’iyyar da karkasuwarta. ‘Yan hamayyar Kwankwaso sun zarge shi da ƙarfa-ƙarfa gami da rashin biyayya ga iyayen jam’iyya. Wanda Hakan ne ma ya sa aka yi masa laƙabi da mai takalmin ƙarfe. Baƙin jinin PDP da kuma Obasanjo ya taimaka matuƙa gaya wajen rikitowar Kwankwaso. Kana kuma uwa-uba matsananciyar ƙishirwar assasa tsarin Shari’ar Musulunci da Kanawa ke yi a wancan lokacin. Shi kuma Kwankwaso sun kalle shi a matsayin wanda ya gaza gudanar da ita ita yadda ya kamata. Duk kuwa da a lokacin ana kama giya, yin bulala ga ‘yan giya da kuma kamen karuwai. Rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP ya ƙara rura wutar rikicin kai Kwankwaso ƙasa.

Wannan ne ya ba wa Malam Ibrahim Shekarau damar zama gwamna har karo na biyu ƙarƙashin jam’iyyar ANPP. Daga 2003 zuwa 2011 wanda hakan ya sa ya kafa tarihi na farko a siyasar Kano da ya maimaita zango mulki biyu a jere. Ibrahim Ali Amin Little shi ne ɗan takarar na farko da jam’iyyar ANPP ta ba wa tutar takara amma kuma daga bisani Buhari da muƙarrabansa suka shiga suka fita suka ƙwace takarar suka ba wa Shekarau. Wanda Hakan ya sa shi ficewa daga jam’iyyar ya ɗauko PRP ya tsaya takarar Gwamna.

Kafin Buhari ya ɗaga hannun Shekarau babu ɗan takarar da ya yi tasiri a wannan lokacin kamar Dan Hassan da ya fito a jam’iyyar PSP. Duk da mahaukatan kuɗaɗen da ya riƙa rabarwa da kuma maƙudan kuɗaɗen da ke hannun Little da gwamnatin da ke hannun Kwankwaso bai hana Shekarau lashe zaɓe ba.

Shekarau ya janyo masarauta da malamai da kuma ma’aikatan gwamnati sun yi yadda suka so a zamanin mulkin sa. Kamar yadda aka zargi wasu kwamishinoninsa da facaka gami da tara mahaukatan kuɗaɗe. An kuma zarge shi da raunin ɗaukar mataki akan duk wanda ya yi babakere da dukiyar al’umma.

Kafin rasuwar Rimi ya soki gwamnatin Shekarau da rashin manufa da kuma babakere. Bugu da ƙari an soke shi da barin matansa sun yi yadda suka ga dama a cikin gwamnati. Kana kuma ya fuskanci tutsu daga jiga-jigan jam’iyyar ANPP ciki kuwa har da jagoranta janar Muhammadu Buhari.

Sakamakon samun saɓani irin na siyasa wanda hakan ya sa Shekarau fuskantar adawa a matsayin wanda ya ci albarkacin Buhari ya kuma bijire masa. Shekarau ya bayar da damar faɗin albarkaci irin na siyasa. Wanda Hakan ya ƙyanƙyashe mutane da dama a matsayin sojojin baka. Waɗanda ba su da aikin komai sai dai a biya su su shiga kafar yaɗa labarai su zagi wanda su zagi wanda su ka so su yabi wanda su ka so.

Kwankwaso ya dawo ta hanyar kafa tarihi a siyasar jihar da ya zama gwamnan da ya bar kujerar mulki har tsawon shekaru takwas sannan kuma ya ƙara dawowa. Lamarin da aka yi wa laƙabi da hannun karɓa hannun mayarwa. Wannan tarihin siyasa da Kwankwaso ya kafa ya zama bai tsaya iya Kano ba domin a ilajirin siyasar Nijeriya babu gwamnan da ya bar kujerar mulki ya kuma dawo bayan shekara takwas. Kana kuma ya zama Gwamna na biyu bayan Rimi da ya assasa muhimman ayyuka a jihar da za a daɗe ana amfana. Ya kuma tsuke bakin aljihun gwamnati ga barin facaka sannan kuma ya takawa ma’aikatan gwamnati birki ga fantamawa da dukiyar talakawa.

Duk da Shekarau na riƙe da akalar gwamnati hakan bai ba shi damar kafa Takai a matsayin Gwamna ba. Bayan kafa jam’iyyar adawa ta APC Shekarau ya zama shi ne jagoranta a jihar Kano, kafin daga bisani Kwankwaso ya dawo jam’iyyar. Wanda hakan ya zama silar tsallakewar Shekarau ya koma jam’iyyar PDP wacce a baya ya ke matuƙar adawa da ita.

Tarihin siyasar jihar Kano abu ne da idan za a rubuta zai ɗauki tsawon lokaci gami da tara tarin litattafai da dama. Siyasa ce mai ɗaure kai da za a iya kira da bauɗaɗɗiyar da ba ta da gwani. Siyasa ce da za a iya kira da hawainiya saboda ta na iya sauyawa a kowane irin lokaci. Siyasa ce ta ra’ayi domin babu wani attajirin ɗan takarar gwamna da ya taɓa yin takara da talaka ya yi nasara a kansa. Kamar yadda wani Gwamna bai taɓa kamala wa’adin mulkinsa ya kawo wani ya gaje shi ba. Kana kuma duk gwamnonin farar hula na jihar Kano babu wanda bai taɓa sauya jam’iyya ba sai marigayi Sabo Bakin Zuwo.

 

Muhimman Abubuwa A Tarihin Gwamnonin Farar Hula Na Jihar Kano

Abubakar Rimi

 • Gwamna na farko a tarihin siyasar Nijeriya da ya sauka daga kan muƙaminsa a yayin da zai sauya wata jam’iyyar.
 • Rimi ya zama gwamnan farar hula na farko a jihar Kano da ya fara zama Ministan Tarayyar Nijeriya. Sakamakon riƙe Ministan harkokin sadarwa da ya yi a lokacin gwamnatin marigayi Sani Abacha.
 • Kana kuma gwamnan farar hula na farko a jihar da ya yi takarar neman shugabancin ƙasa tare da Obasanjo a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP a shekarar 2003.
 • Rimi ya zama gwamnan farar hula na farko da aka kashewa babban dogarin da ke kula da lafiyarsa Dakta Bala Muhammad. Bugu da ƙari gwamnan Kano na farko da aka yi wa matarsa kisan gilla.
 • Gwamna na biyu da ya rasu bayan Sabo Bakin zuwo. Gwamna na farko da ya fuskanci yamutsin rasa rayuka na Maitatsine.

 

Sabo Bakin Zuwo

 • Sabo Bakin Zuwo ya zama shi ne Gwamna mafi rashin daɗewa a karagar mulki a duk cikin gwamnonin farar hula da jihar ta yi.
 • Gwamnan farar hula na farko da ya riga sauran gwamnonin rasuwa.
 • Gwamnan farar hula na farko da har ya rasu bai taɓa sauya jam’iyya ba.
 • Gwamnan farar hula na farko da bai kai sauran gwamnonin zurfin ilimi ba.

 

Kabiru Gaya

 • Kabiru Gaya ya zama gwamnan farar hula na farko a jihar da ya zama Sanata.
 • Shi kaɗai ya taɓa mulki lokacin guda tare da gwamnatin soja.
 • Gwamna na biyu da bai daɗe a bisa karagar Gwamna ba bayan Sabo Bakin Zuwo.

 

Kwankwaso

 • Ya zama gwamnan farar hula na farko a Nijeriya da ya zama Ministan tsaro.
 • Shi ne Gwamna mafi yawan tsayawa takarar siyasa a jihar.
 • Gwamnan da a Nnijeriya shi ya fara tafiya ya dawo bayan shekara takwas.
 • Gwamna na farko da ya fara yi wa jihar jami’a da kuma gadar sama.
 • Gwamna na farko da ya binne marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da duk gwamnonin da jihar ta yi sun shuɗe sun bar shi.
 • Kuma gwamnan siyasa na farko da ya naɗa sabon Sarki.
 • Gwamnan farar hula na biyu da ake kallo a matsayin gardamamme bayan Rimi.
 • Gwamna na farko da jihar Kano ta fuskanci yawaitar kai munanan hare-haren ta’addanci na Boko Haram.
 • Gwamna na farko da ya fara ƙaddamar da tsarin shari’ar Musulunci.
 • Gwamna na farko da ya assasa sunan sa ‘Kwankwasiyya’ a matsayin ɗarikar siyasa.

 

Shekarau

 • Gwamna na farko da ya mulki jihar Kano har sau biyu a jere.
 • Gwamna na farko da ya mulki jihar da mata uku.
 • Gwamna na farko da ya mulki jihar a matsayin mai alaƙanta kansa da siyasar addini.
 • Gwamna na farko a Nijeriya da ya zama Ministan harkokin ilimi ba da matsayin farfesa ba.
 • Gwamna na farko da ya yi takarar shugabancin ƙasa a babban zaɓe.
 • Gwamna na farko da ya yi kuka akan mulki har sau biyu.
 • Gwamna na farko da ya zama Basarake da sarautar Sardaunan Kano.
 • Gwamna na farko da ya yi zamani da shugabannin ƙasa har guda uku. A shekarar 2003 ya yi da Obasanjo, marigayi ‘Yar adua ya riske shi a 2007. Kana kuma ya kamala wa’adin mulkinsa tare da Jonathan.
 • Kana kuma Gwamna na farko a jihar da aka yi wa mashahurin Malami kisan gilla wato marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam.

 

Abdullahi Umar Ganduje APC

Ganduje Gandun Aiki. Shi ne kusan sunan da kowa ya fi sanin sa a jihar Kano. Dakta Abdullahi Umar Ganduje shi ne cikakken sunansa. Kuma shi ne ya kafa tarihin mataimakin gwamna kaɗai a faɗin jihar Kano da ya yi zangon wa’adin mulki har karo biyu. Da shi Kwankwaso ya yi mulkin jihar a 1999 zuwa 2003 bayan ya sake cin zaɓe a 2011 ya sake dawo da shi har zuwa yau. Ganduje ya sake kafa tarihi a siyasar jihar Kano a matsayinsa na mataimakin gwamna da ba a taɓa jin kan su ba. Kana kuma ya na da tarihin shi ne kaɗai mataimakin gwamna a jihar da ya ke da gidauniyar tallafawa al’umma mai suna Ganduje Foundation. An yabe shi a matsayin mai matuƙar haƙuri da juriya gami da iya kyautata mu’amala da mutane. A halin yanzu ‘yan adawa na jifansa da kalmar Ganduje gandun bacci maimakon gandun aiki. Hakan kuwa ya biyo baya ne sakamakon wasu hotunansa da suka karaɗe ko ina ya na zabgar bacci a wajen taro.

Kana kuma ana kallon sa a matsayin mai cutar mantuwar da ba ya iya rabewa da kusan mutanen da ya ke mu’amala da su.

Ganduje ya zama Gwamna na farko a tarihin siyasar jihar da wani Gwamna mai ci ya riƙo hannun sa kana kuma ya yi sa’ar zama Gwamna. Kana kuma a yanzu babu Gwamna da ya ke shan baƙar adawa irin ta siyasa a farkon zangon sa kamar Ganduje.

Ya na fuskantar tsangwama daga tsagin Kwankwasiyya da suke ɗaukarsa a matsayin butulun da ya bijirewa maigidansa. Kana kuma batun haraji masu ababen hawa na daga cikin abinda ya ke neman zame masa ƙadangaren bakin tulu. Bugu da ƙari ya rasa zaƙaƙuran hadiman da za su riƙa yayata manufofinsa.

Har ila yau, wasu na kallon Gwamnan a matsayin marowaci, wanda bay a yin kyauta ga makusantansa.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI