Connect with us

WASANNI

Juyin Juya Halin Da A Ka Fara Samu A Firimiya Ta Nijeriya

Published

on


Daga Taofeek Lawal, Abuja

A tarihin ƙwallon ƙafa za mu iya cewa koda yaushe tsofaffi ne su ke cin karensu babu babbaka, domin a shekarun baya sai ɗan ƙwallo ya kai adadin wasu shekaru kafin a fara kallon sa yana buga ƙwallo a fili.

A nan Najeriya ma abubuwa sun fara canjawa a ’yan shekarun nan, musamman ma a wannan shekarar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Plateau United ta lashe gasar Firimiya ta bana.

Ƙungiyar Mountain Of Fire ta jihar Legas ita ce ta yi ta biyu a gasar kuma dukkaninsu ’yan wasansu matasan ’yan wasa ne masu jini a jika.

Tabbas an fara samun canji a harkar ƙwallon ƙafa a Najeriya domin samari sun fara samun gindin zama kuma sun fara haskakawa hakan ya na nufin dole sai tsofaffi su haɗa kayansu su koma gefe.

A karon farko cikin a tarihin ƙungiyar, Plateau United ta lashe gasar Firimiya ta ƙasa da matasan yan wasa sannan shi kansa mai horar da yan wasan ƙungiyar matashin mai koyarwa ne domin yana daya daga cikin samarin masu koyarwa a kakar wasan data gabata.

Shi kansa shugabancin hukumar ƙwallon ƙafar ta ƙasa za mu ga ya koma hannun matashi duk da cewa ba yaro bane amma zamu iya cewa bai kai shugabannin baya shekaru ba.

Idan mu ka duba a baya bayan nan an samu canji a harkar ƙwallon ƙafa a duniya bayan da tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, Jose Sepp Blatter shi ma ya sauka sakamakon zargin cin hanci kuma aka samu Gianni Infantino yazama sabon shugaba wanda shima bai kai Blatter shekaru ba.

A hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai ma zamu iya ganin canji domin shima Michel Platini ya sauka inda Aleksander Ceferin yazama shine sabon shugaban ƙwallon ta nahiyar turai, a nan Africa ma an samu canji domin a karon farko cikin shekaru sama da goma Issah Hayatou yabar shugabancin hykumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Africa inda aka zabi Ahmad Ahmad a matsayin sabon shugaba.

Za mu iya cewa an fara samun gagarumin canji a harkar ƙwallon ƙafa a duniya gaba daya domin ana samun samari acikin yan wasan ma ko a nahiyar turai da kudancin amurka.

A wasikar taya murna da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ya aiko, Gianni Infantino ya yabawa yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta plateau united da mai koyarwar ƙungiyar da magoya baya da kuma duk wanda ya taimaka ƙungiyar ta samu wannan gagarumar nasara.

Wannan ya nuna yadda aka fara samun canji a ƙwallon ƙafa, tabbas idan samari masu jinni a jika suna shiga za’a samu canjin da ba a za ta ba.

Yanzu dai ƙalubalen da yake gaban shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa shine yayi ƙoƙarin ganin ƙungiyoyin plateau united da Mountain Of Fire da zasu wakilci ƙasar nan a gasar zakarun nahiyar Africa sunyi abin azo agani a wannan shekarar.

A shekarun baya tabbas ƙungiyoyin da suke wakiltar ƙasar nan basa buga abin azo agani a gasar saboda dalili na rashin shiryawa cikin lokaci sannan kuma babu cikakken jagoranci daga hukumomi wajen taimaka musu ta hanyar bibiyar wasanninsu.

Suma gwamnonin jihohin Plateau da legas suna buƙatar su jajirce wajen ganin ƙungiyoyin sunyi abin azo agani a gasar tunda ƙungiyoyin suna hannun gwamnatocin jihohi ne daman.

Misalign ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kano pillars da Enyimba a baya, gwamnatocin jihohinsu sun taimaka musu a gasar zakarun nahiyar Africa sosai ta hanyar bibiyarwasanninsu da kuma goya musu baya da kudin da suke buƙata.

Kamar yadda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta real Madrid take wakiltar sifen ba garin Madrid ba da kuma yadda Chelsea take wakiltar ingila ba London bah aka ƙungiyoyin plateau united da MFM zasu wakilci ƙasa najeriya ba jihohinsu ba, saboda haka akwai buƙatar a hada hannu sosai domin ganin an dawowa da ƙasar nan ƙimar da take da ita a ƙwallon ƙafa musamman a nahiyar Africa.

Tabbas nasan gwamnonin jihohin da wadannan ƙungiyoyi suke zasuyi maraba da shugaba Amoju Pinnick idan har yaje ya nemi hadin kansu domin ganin ƙungiyoyin sun buga abinda yakamata su buga.

Sannan su kansu ƙungiyoyin suna buƙatar fara shiryawa da wuri domin tun karar gasar domin yazama kamar al’adar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a najeriya basa fara shiryawa gasa sai ta tunkaro, yanada kyau su fara shiryawa ta hanyar buga wasannin sada zumunta da manyan ƙungiyoyi na nahiyar turai ko kuma na nan nahiyar Africa wadanda babu kamarsu.

Wannan shine zai bawa ƙungiyoyin damar gane cewa shirin da sukayi yayi ko kuma suna buƙatar sabon shiri, wato ta hanyar buga wasannin sada zumunci da manyan ƙungiyoyi masu ƙarfi sosai.

Wani abin farin ciki shine yadda shugaban na hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa a yanzu yana cikin manyan masu fada aji a hukumar ƙwallon ƙafan ta nahiyar Africa, hakan yana nufin zai iya amfani da tasirinsa a hukumar na ganin ƙungiyoyin namu sunyi abin azo agani ta hanyar bibiyar duk wasu abubuwa da zasu dinga gudana a hukumar musamman a harkar wasannin zakarun African.

Harkar ƙwallon ƙafa a najeriya a halin yanzu tana samun gagarumin canji idan muka duba yadda take a baya, ana samun matasan yan wasa suna shigowa kuma suna haskakawa yadda yakamata sannan kuma su kansu masu horarda ƙungiyoyin ana samun matasa aciki wanda hakan yake nufin nan gaba akwa gagarumin canji.

Bayan kammala gasar Firimiya ta shekarar data gabata yanzu haka ƙungiyoyi sun fara shirye shiryen tunkarar sabuwar gasar da za’a fara nan gaba kadan ta hanyar neman sababbin yan wasa da kuma yin gyare gyare a ƙungiyoyin nasu.

Yanzu an gama wasan Firimiya ta ƙasa, yanzu sai muzo mu hada hannu domin gannin ƙungiyoyin da zasu wakilcemu sun lashe gasar zakarun nahiyar Africa na champions league da kofin Comfideration cup.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI