Connect with us

WASANNI

Na Daina Sha’awar Ƙwallon Ƙafa Tunda Na Koma Liverpool

Published

on


Daga Abba Ibrahim Wada

Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liɓerpool, Poul Lambert ya bayyana cewa lokacin da ya bar Southampton yakoma Liverpool a lokacin ya daina sha’awar ƙwallon ƙafa a rayuwarsa.

Lambert, wanda ya koma Liverpool daga Southampton a shekara ta 2014 ya yi ritaya daga buga ƙwallo ne a kwanakin baya sakamakon ciwo da ya yi fama da shi wanda ya hana shi buga wasanni a kai-a kai.

Ɗan wasan ya taka rawar gani a Southsmpton inda yazura ƙwallaye 117 a tarihin zamansa a ƙungiyar kafin daga baya yakoma Liɓerpool, ƙungiyar da yafara tun yana ƙoƙari.

Dan wasan yace, yabar Southampton yakoma Liverpool duk da cewa yasan babu lallai ya dinga bugawa a ƙungiyar, amma sai dai daman kociyan Liɓerpool din na wancan lokaci Brendan Rodgers yayi masa alƙawarin cewa dole bazai dinga buga wasanni kullum ba,

Lambert dai yabuga wasanni 36 a Liverpool sannan ya bugawa ƙasar sa ta ingila wasanni 11 inda yaci ƙwallaye uku.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI