Connect with us

WASANNI

Rooney Ya Fara Aiwatar Da Hukuncin Kotu Na Shuka Fulawa

Published

on


Abba Ibrahim Wada

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ɗan wasan Manchester united, Wayne Rooney, ya fara aikin shuka fulawa kamar yadda wata kotu a ƙasar Ingila ta umarce shi da ya yi bayan da ta yanke ma sa hukunci sakamakon kama shi da a ka yi ya na tuƙa mota bayan ya na cikin maye.

A farkon watan Satumba ne dai yan sanda a ƙasar ingila suka kama dan wasan acikin mota yana cikin giya inda bayan sun kamashi suka gabatar dashi agaban kotu inda kuma kotun tayi masa hukuncin aiki acikin unguwa na awanni dari sannan kuma aka hanashi tuƙa mota na tsawon shekaru biyu bayan tarar da zai biya.

Tuni dai dan wasan, wanda yakoma tsohuwar ƙungiyarsa ta eɓerton ya amsa laifinsa agaban kotun kuma yabawa magoya bayan da iyalinsa da shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta eɓerton haƙuri sakamakon laifin daya aikata.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana tuni dan wasan yafara aikin shuka fulawa a yankin da yake zaune domin ƙawata garin sannan kuma zai cigaba da kulawa dasu har na tsawon awanni dari.

A kullum dai dan wasan zai dinga shafe awanni shida yana wannan aiki kamar yadda kotun ta tsara masa.

Dan wasan dai ya zura ƙwallaye uku cikin wasanni 13 daya bugawa eɓerton din tun bayan daya ƙungiyar a cikin watan agustan daya gabata.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI