Connect with us

WASANNI

Sharhin Bundes Liga

Published

on


Abba Ibrahim Wada

Gasar Bundes Liga an fara tane a shekarar 1963 zuwa 1964, kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern munchen itace tafi kowacce ƙungiya lashe gasar sau 26, sannan kuma har ila yau ƙungiyar itace take jagorantar ƙungiyoyin da suke buga gasar.

Sai dai a wannan shekarar kusan zan iya cewa abubuwa sun canja musamman a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich duba da yadda ƙungiyoyi irinsu Borussia Dortmund da FC Leifzieg suka yunƙuro domin ƙalubalantar Bayern din.

Zuwa yanzu dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Dortmund ce take kan gaba a gasar bisa yadda tafara buga gasar da ƙafar dama duk da cewa ta siyar da shahararren dan was anta Ousman Dembele zuwa Barcelona.

A satin daya gabata ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern munchen ta kori mai koyarwarta Carlo Ancelotti duk da cewa ya lashe gasar a kakar wasan data gabata.

Ƙungiyar ta Bayern munch dai kusan zance suna cikin mawuyacin hali a halin yanzu `domin wadda take matsayi na daya wato Borussia Dortmund ta bata tazarar naki biyar kuma yanayin yadda dortmund din take buga wasa zamu iya cewa ƙungiyar ta samu kanta.

Bayern munich ce take binta a baya sai dai itama Hoffeeinhaim itace take bin munich din a baya kuma tazarar ƙwallaye ce a tsakaninsu.

Itama leifzieg tazarar maki daya ne kawai tsakaninta da Bayern munich din wanda hakan yake nufin babu wata tazara babba tsakaninta da wadannan ƙungiyoyi da suke binta a baya.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta RB Leipzig ce ta taka rawar gani sosai a kakar wasan data gabata inda kusan zamu iya cewa itama ta sakawa munich ciwon kai.

Wani abu sabo a ƙungiyar ta Bayern munich shine yadda aka rufe kasuwar siyan yan wasa amma basu siyo sababbin yan was aba kuma ƙwararru banda James Rodriguez wanda shima aro suka karbo shi daga real Madrid.

Gasar bundes liga dai kusan zan iya cewa ta mai rabo ce a wannan shekarar duba da yadda babu wata ƙungiya da za’ace tafi ƙarfin wata.

Abin jira a gani dai yanzu shine ko ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern munich zata iya farfadowa duba da har yanu ba’ayi nisa a wannan kakar ba, sannan kuma ita kungiyar ƙwallon ƙafa ta Borussia Dortmund zata iya jurewa har ƙarshen kakar a matsayi na daya, shin itama RB Leipzig zata iya jure gasar zakarun turai da wasannin bundes liga?

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI