Connect with us

WASANNI

AC Milan Za Ta Taya Aguiro Idan Sanches Ya Koma Mancity

Published

on


Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan ta bayyana aniyarta ta neman ɗan wasan gaba na Manchester City, Sergio Aguiro idan har Alexis Sanches ya koma City.

AC Milan dai a shirye take data kashe kuɗi domin sayen ɗan wasan wanda ta neme shi a watan Agustan daya gabata inda Manchester City ta ce bana sayarwa bane.

A kasuwar saye da sayarwar ‘yanwasa data gabata dai AC Milan ta kashe kuɗi wajen ƙara ƙarfin ƙungiya saboda ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen sababbin ‘yan wasa kuma matasa.

Manchester City dai tana buƙatar sayen Alexis Sanches, inda ɗan wasan yakusa komawa ƙungiyar a ƙarshen watan Agusta, daya gabata kafin daga baya cinikin ya rushe sakamakon Arsenal bata samu wanda zai maye gurbinsa ba.

Sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewar Manchester City za ta koma neman ɗan wasan a watan Janairu saboda ta sake gwada Arsenal akan kuɗi fam miliyan 25.

Rahotanni dai sun bayyana cewar mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola yana buƙatar matashin ɗan wasan gaba, inda hakan yake nufin zai iya rabuwa da Aguiro idan har yasamu ɗan wasan dayake so.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI