Connect with us

WASANNI

Na Kusa Yin Ritaya In Bar Wa Iwobi Lamba Goma – Mikel Obi

Published

on


Kaftin ɗin tawagar yan wasan Nijeriya ta super eagles, Mikel Obi ya bayyana cewa nan bada jimawa ba zaiyi ritaya daga buga ƙwallo kuma sannan zai barwa Aleɗ Iwobi riga mai lamba goma domin yacigaba da sakawa.

A hirarsa da manema labarai, Alex Iwobi, wanda shine yaciwa Nijeriya ƙwallonta daya wadda tabata damar samun tikitin zuwa ƙasar rasha, an tambayeshi ko yanada sha’awar saka riga mai lamba goma ganin dan uwansa, tsohon dan wasan ƙasar nan Jay-Jay Okocha shima yasaka rigar.

Iwobi ya bayyana cewa baya buƙatar maganar riga mai lamba goma a halin yanzu domin kaftin dinsa ne yake sakawa kuma yanzu buƙatarsa kawai shine a samu nasara aƙasar rasha.

Dan wasan yacigaba da cewa bai damu da saka riga mai lamba goma ba domin bata gabansa, abinda yake gabansa kawai shine samun nasarar ƙasar nan, sannan yace yana alfahari da saka rigar ƙasar nan.

Sannan yace dan uwansa Okocha bai takura masa akan sai yasaka riga mai lamba goma ba saboda haka komai lokaci ne idan yanada rabo wataran zai saka ta a jikinsa.

Dan wasan dai yana bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta arsenal ne ta ƙasar ingila kuma bai buga wasanni biyun da Nijeriya ta fafata da ƙasar kamaru ba sakamakon ciwo dayayi fama dashi a kwanakin baya.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI