Connect with us

WASANNI

Neymar Na Son EUFA Ta Kori Barcelona Daga Champions League

Published

on


Tsohon dan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Neymar jr ya buƙaci hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai data kori Barcelona daga gasar zakarun turai indai ƙungiyar bazata biya mahaifinsa haƙƙinsa ba.

Neymar dai yabar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona yakoma PSG akan kudi fam miliyan 200 a kasuwar siye da siyar da dan wasan data gabata sai dai tun lokacin da dan wasan yabar Barcelona ake samun matsaloli na cece kuce tsakaninsa da ƙungiyar bayan da Barcelona taƙi biyan mahaifin dan wasan kudinsa fam miliyan 23.

An ruwaito cewa dan wasan ya sanar da lauyansa cewa ya dauki mataki na shari’a akan tsohuwar ƙungiyar tasa sannan kuma yayi kira ga hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai data kori Barcelona daga kofin zakarun turai.

Sai dai tuni hukumar ta Eufa ta fahimci buƙatar Neymar din inda tayi fatali da buƙatar dan wasan kuma tace wannan ba hurumin dan wasan bane kuma basuyi laifin da za’a koresu ba.

Sai dai itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona takai Neymar din ƙara kotu inda ta buƙaci daya biyata kudadenta data bashi lokacin da yasake sabon kwantaragi dasu.

Neymar dai yaci kwallaye 105 a Barcelona a wasanni 186 sannan kuma a halin yanzu yazura ƙwallaye takwas a cikin wasanni takwas daya buga a PSG din.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI