Connect with us

RA'AYINMU

Yaushe Za A Daina Zubar Da Jini A Nijeriya?

Published

on


Akwai matuƙar tashin hankali yadda kullum ake  samun yawaitar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a babu gaira babu dalili a ƙasar nan, musamman bisa la’akari da irin asarar da rikice-rikice ke janyo wa ƙasar nan. Waɗannan kashe-kashe suna neman fito da maitar wasu ‘yan Nijeriya fili kan buƙatarsu ta zuƙar jinainan ‘yan uwansu, wanda hakan ke jefa ayar tambaya kan imaninmu da ɗan’adamtarmu. Lamarin har ya kai munzalin da shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari abun ya ɗaure masa kai, yana kokwanto anya ‘yan Nijeriya sun san darajar ɗan’adam kuwa.

Tsakanin ‘yan shekarun da suka gabata, babu wata rana da ta wuce ba tare da ɓullar rahoton an kashe wani ko wata ba, kisa wanda ya wuce hankali. Hanyoyin da waɗannan mugaye ke bi wajen aikata ta’asa abin tsoro ne matuƙa, ba su da imani daidai da cikin cokali. Sun mayar da ‘yan uwansu tamkar dabobi, a wasu lokutan ma dabba ta fi ‘yan uwansu daraja; a wurinsu, yin gunduwa-gunduwa da gangar jikin maƙwabtansu ba wani abu ba ne; su kashe; su bizne, su daddatsa; su watsar kan tituna sannan kuma riƙa murnar irin ɓarnar da suka yi a bayyane. Shin yaushe za a daina zubar da jinin ‘yan Nijeriya ne?

Waɗannan kashe-kashe sun ɗauki sabon salo tun bayan dawowar tsarin mulkin dimukraɗiyya sakamakon tsagerun matasa da ‘yan siyasa ke amfani da su a matsayin masu kare tawagarsu daga harin ‘yan adawa. Suna ba su mamaki da miyagun ƙwayoyi su yi abin da suka ga dama har zuwa lokacin zaɓe. Inda gizo yake saƙar shi ne, bayan zaɓe sai a bar su da makamai a hannu ba tare da an karɓe ba, su kuma tun da ba saiti ke garesu ba, kan wata biyan buƙatarsu kansu, sai su zama jagororin kansu, ba kwaɓa balle faɗa. Da yawan mutane sun tafi a kan wannan shi ne jijiyar da ta yi sanadin ɓullar bishiyar da ta yi ganyen ta haifar da ‘ya’yan ƙungiyar Boko Haram, waɗanda cikin ƙanƙanin lokaci suka addabi Nijeriya da duniya baki ɗaya.

Sojoji na tsaka da fatattakar waɗancan masu tayar da ƙayar bayan, sai kuma ga shi wasu nau’ukan makasan sun sake ɓulla da sunaye kala-kala; ‘Yan Bindiga ko kuma Fulani Makiyaya, inda suke neman ture waɗancan su kafa nasu sansanin shan jinin jama’a. Suna kai farmaki, su kashe na kashewa su raunata na raunatawa, idan hali ya yi kuma su sace mata da tsaffi. Baya ga wannan, ga rikicin ƙabilanci da yake shirin samun gindin zama, har yanzu kuma ba a ɗauko hanyar daƙile shi ba.

A duk waɗannan rikice-rikice da ake yi, ba ɗaiɗaikun mutane ne ke mutuwa ba, a’a, ɗaruruwa ne ko a ce dubbai kuma ba yaƙi ake yi da wata ƙasa ba, balle a ce. Jami’an tsaro sun bayyana masu aikata waɗannan laifuka a matsayin ‘ɓata-gari’ waɗanda suke son tada zaune tsaye, amma babu koda mutum guda da aka kama balle a gurfanar da shi gaba kuliya.

Mun ga dacewar fito da abubuwa fili, cewar Gwamnoni Jihohi suna karɓar kaso mai tsoka daga Gwamnatin Tarayya da sunan Tsaro. Akwai rundunonin ‘Yan Sanda, Jami’an Tsaro, Sansanin Soji da sauran jami’ai masu ɗamara. Amma duk da waɗannan sun gaza daƙile kashe-kashen da ke ci gaba da yawaita a cikin al’umma tamkar sun mance da haƙƙinsu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa bisa alƙawari da suka yi.

Kafin yanzu, mafi yawacin zarge-zargen da jami’an tsaro ke yi shi ne cewar, masu kai farmakin ba ‘yan Nijeriya ba ne, suna sulalowa ta iyakokin ƙasa, su yi ɓarna sannan su fice. Idan har ta tabbata haka ne baƙi na kawo wa ‘yan ƙasa hari, to lallai ana buƙatar mutumin da zai jagorancin yaƙi da wannan rashin hankalin.

Mun fahimci ‘yan Nijeriya da yawa suna da ra’ayin cewa jami’an tsaro sun gaza matuƙa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, wanda hakan a kullum yake ƙara zubarwa da ƙasar mutunci a idon duniya. Ƙasashen Duniya, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya suna kokawa matuƙa kan kashe-kashen babu gaira babu dalili a Nijeriya.

Shugaba Ƙasa ya yi wata ganawa ta musamman da Shugabannin Tsaro kwanakin baya don su yi masa bayanin matakan da suke ɗauka wajen shawo kan waɗannan rikice-rikice. Fatanmu shi ne, hukumomi su yi mai yiwuwa don tabbatar da ganin an dawo da martabar ran ɗan’adam. Halin da ake ciki a yanzu na rashin yarda da aminci tsakanin ƙabilu, lallai ya dace gwamnati ta yi wani abu, domin zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki!

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI