Connect with us

MANYAN LABARAI

Aisha Buhari Ta Caccaki Asibitin Fadar Gwamnati

Published

on


Daga Mustapha Hamid, Abuja

A jiya Litinin, Matar Shugaban Ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta yi dirar mikiya akan hukumar asibitin fadar shugaban ƙasa ‘State House Medical Centre’, inda ta zarge su da rashin yin abin da ya dace.

Matar shugaban ƙasan ta bayyana cewa, akwai ban mamaki ganin shirin da hukumar asibitin ke yi na sabbin gine-gine dag yare-gyare a asibitin, alhali hatta magani mafi rahusa babu, kayan gwaji da sauransu gaba ɗaya basu aiki.

Aisha Buhari ta faɗi haka ne a wurin taron yini guda na masu ruwa da tsaki dangane da lura da ɓangarorin kiwon lafiya da suka haɗa; haihuwa, jarirai, ƙananan yara, da kuma kumarin matasa, wanda ke ƙarƙashin kulawar shirinta na ‘Future Assured’; shirin da dukkan matan gwamnonin Nijeriya ke cikinsa da wasu masu ruwa da tsaki.

Matar Shugaban Ƙasan ta bayyana yadda a makonni kaɗan baya ta kamu da rashin lafiya, inda ta buƙaci da a yi mata magani a asibitin fadar shugaban ƙasa. Ta ce, asibitin ya bata kunya, musamman yadda suka kasa yi mata maganin rashin lafiyar da ke damunta. Ta bayyana cewa, a lokacin da rashin lafiyar ta same ta, sai ta tuntuɓi wannan asibiti wanda an samar da shi ne don ya kula da lafiyar shugaban ƙasa, iyalansa da sauransu. Ta ce, amma abin ban haushi, hatta injin da za a yi mata gwaji ba ya aiki.

Ta ce, ‘yan Nijeriya na da alhakin a sanar dasu inda kuɗaɗen da ake warewa don siyo kayayyakin asibitin suke tafiya.

Ta ce: “Kafin na fara jawabi kana bin da ya haɗa mu a wannan wuri, zan so na yi tsokaci akan haƙiƙanin abin da ke faruwa a sashen kiwon lafiyan Nijeriya.

“Sai dai a yi min afuwa, amma lamarin dai ba daɗin ji. Na ji daɗi kasantuwar Babban Daraktan asibitin fadar Shugaban Ƙasa yana nan tare da mu. Shin yana nan (Dakta Munir) ko wakilinsa. Yawwa yana ma nan.

“Yawwa Dakta Munir, na ji daɗi kasantuwar kana nan. Sanin kowa ne cewa a watanni shida da suka shuɗe, Maigidana ya yi fama da rashin lafiya. Mun gode wa Allah ya samu lafiya.

“Idan har wani mutum mai matsayin shugaban ƙasa zai kwashe watanni baya ƙasa, saboda neman magani. Sai mu tambayi kawunanmu shin ya talakawa ‘yan ƙasa za su yi.

“Makonni kaɗan baya, na ziyarci asibitin saboda bana jin daɗi. Amma sai suka shawarce ni wai in bi jirgi zuwa Landan. Ni kuma na tubure akan ba zan je ba a nan cikin gida nake so a yi min magani, domin ai akwai kuɗaɗen da aka ware domin kula da lafiyarmu.

“Idan miliyan 100 aka ware wa asibitin, za mu so mu san yadda hukumar asibitin ta kasafta kuɗin. Da na cije akan sai sun kira jami’an asibitin don a duba ko injin gwajinsu na aiki, sai suka ce min ai baya aiki. Wannan ya tilasta min zuwa wani asibitin kuɗi wanda yake mallakin wasu ‘yan ƙasashen waje ne. wannan me yake nufi?

“Ina ganin ya kamata mu san me mu ke yi. Idan har irin haka za ta faru da ni a Babban birnin Tarayya, Abuja, babu buƙatar ma na fara tambayar matan gwamnoni dangane da abubuwan da ke faruwa a jihohinsu. Nan fa Abuja ne, gari mafi ƙima a tarayyar Nijeriya, kuma wannan lamari ya faru ne a asibitin fadar shugaban ƙasa.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI