Connect with us

RA'AYINMU

Har Yanzu Kan Buƙatar Muhimmanta Waziran Makarantu

Published

on


A makon jiya mun fara bayani a kan muhimmancin aikin waziran makarantu a ɗaukacin makarantun da muke da su a ƙasar nan musamman makarantun gwamnati waɗanda ba su cika mayar da hankali a kai ba saɓanin masu zaman kansu.

Ƙasashen duniya da suka cigaba, sun lura da muhimmancin waɗannan wazirai, shi ya sa ba su yin sako-sako da su a makarantunsu. A ƙasar Japan, waziran makarantu suna taimaka wa ɗalibi ya fahimci kansa (wurin da yake da ƙarfi da ɓangren da yake da rauni), ya zama mai ra’ayin kansa, ya iya tsara rayuwarsa da irin matakan da zai bi ya gyara tarnaƙin da ka iya masa barazana ga cimma burinsa. A Faransa kuwa, wacce ta fara amfani da waziran a makarantun sakandare a 1922 sannan ta yi cikakken shigar da su cikin tsarin iliminta a 1930, ta wajabta yin aiki da waziri a kowace makaranta. Ita kuwa ƙasar Tailan, malaman da ke koyarwa a makarantu akan horas da su aikin wazirci a makaranta. Ƙasar Honkon, ta tabbatar da aikin wazirin makaranta a ɗaukacin cibiyoyinta na ilimi. Sauran ƙasashe irin su Andulus (Spain), Fotugal, Danmak, Beljiyom, Italiya, Jamhuriyar Silobakiya da Nowai sauran su, sun samar da shafuka na musamman a intanet da al’ummar ƙasarsu ke amfana da waziran. Amma mu a Nijeriya, ina aka bar mu?

Waziran makarantu suna taimaka wa ɗalibai su zama masu ƙwazo. Masana ne akan basira da kaifin ƙwaƙwalwar kowane ɗalibi. Sun fahimci yanayin muhallin karatun da ya fi dacewa da kowane ɗalibi. Waziran makarantu suna yauƙaƙa zumunci da fahimtar juna a tsakanin malamai da iyayen yara, kana sukan daidaita tunanin ɗalibi ya fuskanci burin da ya tasa a gaba.

Galibin matsalolin da suke hana mu sakat a ƙasar nan a wannan zamanin za a iya magance su tun a matakin makarantun sakandare. Saboda a nan ake cusa wa yara irin ɗabi’un da ake son gani a tare da su idan girmansu ya kai isa-matuƙa. Babbar hanyar hakan kuwa ita ce ita ce tabbatar da samar da waziran makarantu a dukkan makarantun sakandare. A matsayinsa na ƙwararre, wazirin makaranta  yana da ƙwarewar da zai hana ɗalibai mu’amala da ɓata-garin abokai cikin ruwan sanyi, ya hana tserewar yara daga makaranta, ya daƙile yawaitar ɗaukan juna biyu a tsakanin ‘yanmata masu tashen balaga a makarantu, ya raba matasa da ɗabi’ar shaye-shaye wadda ta zama ruwan dare a manyan makarantunmu da ƙanana. Bugu da ƙari, duk jami’in da aka horas a fannin kuma ya horu horuwa, yana da ƙwarewa wurin rigakafin tayar da zaune-tsaye a makarantu, da kawar da ƙyamar juna a tsakanin jama’a da kuma tabbatar da zaman lumana da aminci duk da bambancin ƙabila da addini. Har ila yau, ya san hanyoyin rigakafin hana mugun hali samun mazauni a cikin zukata, wannan yana da matuƙar tasiri a wurin ɗaliban da rayuwarsu ta gaba, kasancewar ‘kara tun yana ɗanye ake tausa shi; idan ya bushe sai dai ya karye!

Har ila yau, aikin waɗannan jami’ai ba zai tsaya a makarantu ba kawai, a duk inda suke al’ummar da ke yankin za su amfana da ƙwarewar jami’an wurin taimaka musu su magance matsalolin zamantakewa kamar saɓani a tsakanin mata da miji, tarzoma a tsakanin ‘yan’uwa da kuma sulhu a tsakanin mutanen da ke husuma da junansu. Kenan, idan aka tabbatar da su a makarantu, za a harbi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ga gyara halayyar ɗalibai da ɗora su a kan turbar cimma burin rayuwarsu na alheri da kuma kawo sulhu da zaman aminci a tsakanin al’umma, wanda babban sinadari ne wurin gina ƙasa da al’ummarta.

Idan an muhimmanta aikin waziran makarantu tare da shigarsu cikin tsarin ilimi na gwamnati, za a samu sauƙin ɓarayin gwamnati da magoya bayan masu wargaza ƙasa ta hanyar ta’addanci ko tawaye, kasancewar hatta yaran da suke fita daga makarantu ba tare da sun kammala ba, jami’an suna da ƙwarewar da za su ɗora su a turba mai kyau na koyon sana’o’in da suka dace da su.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI