Connect with us

MANYAN LABARAI

Barin Takarar 2019 A Arewa: Ƙusoshin PDP Sun Yi Wa Abuja Ƙawanya

Published

on


  • Hayaniya Kawai Fayose Ke Yi –Jerry Gana
  • A shirye Nake Na Sadaukar Da Raina –Wike

Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

A yayin da zaɓen shekarar 2019 ke sake ƙaratowa da gabatowar zaɓen shugaban jam’iyyar PDP; jiya gamayyar wasu shugabanni da dattawan jam’iyyar PDP na arewa sun yi wa Babban Birnin Tarayya, Abuja ƙawanya. Waɗannan shugabanni da dattawa sun fito ne daga jihohin arewa 19 ciki har da Babban Birnin na tarayya, inda suka tattauna wasu muhimman batutuwa, ciki hard a batun barin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ga arewacin Ƙasar.

Taron wanda aka gudanar bisa jagorancin Farfesa Jerry Gana, wanda memba ne majalisar amintattun jam’iyyar, sun ƙara jaddada cewa takarar shekarar 2019 na arewa ne, su kuma kudanci su samar da shugaban jam’iyya, a babban taron jam’iyyar da za a gabatar a watan Disamba mai zuwa.

Ƙusoshin jam’iyyar sun jaddada cewa babu wani abu da zai hana tabbatar yarjejeniyar barin takarar shugaban ƙasa a arewa, wanda aka cimma matsaya kwanakin baya a garin Fatakwal.

Cikin waɗanda suka samu halartar wannan taron, kuma suka tofa albarkacin bakinsu akwai Sanata Jubril Wali, Shugaban majalisar Amintattu, Sanata Maƙarfi, Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar Sanata Ahmadu Ali, tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP, Dakta Halliru Bello, tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Iyochi Ayu, tsohon shugaban majalisar dattawa, Alhaji Kabiru Turaki, tsohon minister, Ambasada Fideliɗ Tapgun da dai sauransu.

Shugaban taron, kuma tsohon ministan yaɗa labarai, Farfesa Jerry Gana a jawabinsa na maraba da baƙi, ya bayyana cewa akwai buƙatar ‘ya’yan jam’iyyar su yi iya yinsu wurin zaɓen nagartaccen mutum a matsayin ɗan takara.

Ya ce; “Ɓaɓatun da gwamna Fayose yake yi a kwanakin nan, ba komi bane banda hayaniya, kuma wannan ba zai hana barin takarar shugabancin ƙasa a arewa kamar yadda aka cimma matsaya.

“Ina roƙonku da ku ƙoƙarta wurin yin amfani da wannan dama da aka bamu na fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa. Mun tsayar da mutumin da zai karɓo a wurin al’umma. Bai kamata mu riƙa ɓata lokacinmu wurin tankawa mutane irinsu Fayose ba, tunda wannan matsaya ce da uwar jam’iyya ta cimma wa.” Inji shi

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban riƙon ƙwaryar jam’iyyar, Sanata Ahmed Maƙarfi ya yaba da irin sadaukarwar da mahalarta taron suka nuna, musamman bisa la’akari da irin yadda suka baro garuruwansu zuwa Abuja domin halartar wannan taro. Suka kuma ɗauki ɗawainiyar kawunansu na wuraren kwana, da abinci. Maƙarfi ya ce, wannan ba ƙaramar sadaukarwa bace suka nuna ga jam’iyyar PDP.

Day a juyo kan batun barin takarar shugaban ƙasa a Arewa kuwa, Maƙarfi ya ce; “Taron da aka yi a Fatakwal har yanzu da shi za mu riƙa kafa hujja, kuma matsayar da aka cimma a taron shi ne na rarraba lamarin takara a yankunan ƙasar nan.” Inji Sanatan

A wata sabuwa kuwa, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa a zaɓen 2019 sai dai a yi kare jinni, biri jinni. Za a gwabza bakin rai, bakin fama har sai sun tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta kawo kujerar shugaban ƙasa.

Wike wanda ya bayyana haka wata tattaunawa da yayi da mujallar ‘The Interɓiew’ wacce ake bugawa wata-wata. Ya ce; “Ko da gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakin kashe mu ne, babu damuwa. Domin mun san suna da wasu mugayen ƙulle-ƙulle da tuggu iri-iri. Idan lokacin gwabza wa yayi, mu ma fitowa za mu yi da ƙarfinmu, ko da kuwa hakan na nufin na sadaukar da raina ne.” inji shi


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI