Connect with us

WASANNI

FIFA Ta Ware Sunayen Yan Wasa 30 Domin Lashe Kyautar Gwarzon Ɗan Ƙwallon Duniya

Published

on


Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta ware sunayen yan wasa 30 waɗanda acikinsu ne za’a  fitar da gwarzon ɗan wasan dayafi bajinta a wannan shekarar da muke ciki.

Yan wasan ana fitar dasu ne sakamakon ƙoƙarin da kowanne yakeyi a ƙungiyarsa da kuma ƙasarsa inda yan wasan da suke buga wasa a ƙasar Spaniya sukafi yawa.

Ɗan wasa Cristiano Ronaldo da messi da kuma Neymar sune waɗanda suke kan gaba wajen lashe kyautar, yayinda shima Edin Hazard na Chelsea da takwaransa N’Golo Kante da Harry Kane na Tottenham da Daɓid De Gea suma suka shiga ciki.

Kyautar dai ana bayar da ita ne gad an wasan dayafi bajinta daga watan janairu na kowacce shekara zuwa watan disambar shekarar.

Leonel Messi da Cristiano Ronaldo sune suka lashe kyautar sau tara ajere a tsakaninsu yayinda messi ya lashes au biyar sai Ronaldo mai guda hudu kuma ana saran wannan shekarar ma daya daga cikinsu ne zai lashe kyautar.

Wasu zababbun yan jaridu ne dai yanzu suke zaben wanda zai lashe kyautar tun bayan da hukumar da take kula da bayar da kyautar ta ƙasar faransa da hukumar FIFA suka raba gari.

Ga yadda cikakkun sunayen yake

Aubameyang (Dortmund) benzema (real Madrid) buffon (juɓentus) caɓani (PSG) Coutinho (Liɓerpool) keɓin De Bruyne (man city) daɓid de gea (man united) Paulo Dybala (juɓentus) Edin Dzeko (Roma)Falcao (Monaco) Antoine Griezman (A.masdrid) matt hummels(Bayern munchen) harry kane ( Tottenham) N’Golo Kante (Chelsea) Toni Kroos (real Madrid) Robert Lewandowski (Bayern munchen) Sadio Mane (Liɓerpool) marcelo (real Madrid) Torres (A.madrid) Messi (Barcelona) modric (real Madrid) Neymar (PSG).

Sauran sun haɗa da Jan Oblak (A.madrid) Sergio Ramos (real Madrid) luis Suares (Barcelona) Edin Hazard (Chelsea) Cristiano Ronaldo (real Madrid) Leonardo Barnucci (AC.Millan) Kylian Mbappe (PSG) sai kuma Isco daga real Madrid.

Zadai a sanar da wanda ya lashe kyautar ne a ranar 23 ga watan Oktober na wannan shekarar.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI