Connect with us

WASANNI

Manchester City Za Su Fara Zawarcin Messi

Published

on


Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona tayi wata tattaunawa da wakilan ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Leonel Messi akan ko zai koma ƙungiyar a watan janairu mai zuwa.

A farkon wannan shekarar ne dai aka bayyana cewa ɗan wasan, mai shekaru 30 ya amince da sabon kwantaragin da ƙungiyar tayi masa inda shugaban ƙungiyar ya sanar da cewa tuni angama yarjejeniya tsakanin Messi da Barcelona.

A yanzu dai kwantaragin ɗan wasan a Barcelona bai kai shekara day aba inda tuni aka fara rade radin cewa zai iya barin ƙungiyar nan bada dadewa ba.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester city tayi shirin kasha manyan kudade domin ganin ta dakko ɗan wasan daga ƙasar Spaniya sakamakon tsohon kociyan ɗan wasan, pep guardiola shine yake koyar da ƙungiyar ta manchester city a daidai wannan lokaci.

Sai dai shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Jose Maria Bartemeu ya bayyana cewa ɗan wasan da iyalansa suna cikin farin ciki a garin na Barcelona saboda haka babu inda ɗan wasan zashi.

Manchester city dai tanason kasha kudin dayafi wanda PSG ta kasha ta siyi Neymar daga Barcelona inda ake tunanin zasu taya Messi kusan yuro miliyan 400 kwatankwacin fam miliyan 365.

Messi dai ya fara kakar wannan shekarar da ƙafar dama inda a halin yanzu ya zura ƙwallaye 13 a cikin wasanni tara.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI