Connect with us

WASANNI

Neymar Ya Roƙi PSG Ta Siyo Coutinho

Published

on


Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Neymar jr ya roƙi ƙungiyarsa ta Paris Saint German data siyo ɗan wasan Liɓerpool, Philliph Coutinho domin yakoma PSG din da taka leda.

Barcelona dai taso ta siyi coutinho a kasuwar siye da siyarwar yan wasan da aka rufe a watan agustan daya gabata inda Liɓerpool din ta dage cewa dan was anta bana siyarwa bane.

Sai dai rahotanni sun bayyna cewa PSG din sun nuna sha’awar su akan ɗan wasan, dan ƙasar Brazil domin su haɗa shi da takwaransa Neymar.

Barcelona dai takai tayin kudi har sau uku akan ɗan wasan amma Liɓerpool tace bana siyarwa bane inda sakamakon hakan yasa taje ta siyo Ousman Dembele daga Borussia Dortmund ta ƙasar jamus.

Tun bayan da ɗan wasa Neymar yabar Barcelona dai maganganu marasa dadi suke fitowa daga bangarorin biyu inda kowanne bangare yake zargin daya bangaren

Neymar din dai a kwanakin baya lokacin da yana Barcelona yataba cewa nan gaba zasu iya buga ƙwallo tare da Coutinho din a ƙungiya daya.

Coutinho dai yabuga wasanni uku a Liɓerpool a wannan shekarar inda ya zura ƙwallaye biyu bayan yadawo daga jinyar da yayi sakamakon ciwo dayaji a bayansa.

Har ila yau coutinho din yabi sahun Neymar da messi  da Hazard da Ronaldo a cikin jerin yan wasa 30 da hukumar FIFA ta ware domin zaben  gwarzon wannan shekarar,


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI